Sojoji Sun Yin Zargin Zagon-Kasa a Cikin Harin Da Aka kai Wa Dakarunsu a Abuja

Sojoji Sun Yin Zargin Zagon-Kasa a Cikin Harin Da Aka kai Wa Dakarunsu a Abuja

  • Alamu masu karfi na nuni da cewa harin da aka kai wa dakarun sojoji na Guards Brigade akwai zagon-kasa a ciki
  • Yan bindiga sun kai wa dakarun sojoji na Guards Brigade harin kaunatar baunalokacin da suke sintiri a hanyar Kubwa zuwa Bwari a birnin Abuja
  • Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bayar da umarnin a tsaurara matakan tsaro a babban birnin tarayya Abuja

Abuja - Alamu masu karfi na nuni da cewa harin da aka kai wa sojoji na Guards Brigade da ke sintiri na musamman a yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja, da zagon-kasa a ciki.

News Telegram ta ruwaito cewa, majiyoyin soji da na tsaro, wadanda suka yi magana kan sharadin a sakaye sunansu, sun yi zargin cewa harin da aka kaiwa sojojin akwai zagon kasa a ciki, saboda dakarun Guards Brigde suna da mafi kyawun horarwa a cikin sojoji.

Kara karanta wannan

Fargabar kai hari fadar Buhari: IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

An yi wa manyan sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri a hanyar Kubwa zuwa Bwari a babban birnin tarayyar Najeriya, lamarin da ya haifar da fargaba da firgici a tsakanin mazauna garin.

Guards
Sojoji Sun yi Zargi da Zagon-Kasa a Harin Da Aka kai Wa Dakarun Guards Brigade Legit.NG
Asali: Twitter

Bari in faɗa muku gaskiya babu yadda za ayi ace babu zagon ƙasa a cikin abin da ya faru da dakarun sojojin mu na guards, saboda suna da mafi kyawun horo cikin sojoji kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin da ake ciki, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bayar da umarnin a tsaurara matakan tsaro a babban birnin tarayya Abuja domin dakile harim yanta’ada.

A wata sanarwa a ranar Talata, 26 ga watan Yuli, mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce IGP ya tuhumi hukumar leken asiri ta rundunar da ta hada kai da mazauna yankin domin kakkabe yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Runduna ta yi martani kan harin 'yan bindiga suka kai kan jami'an fadar shugaban kasa

Rashin tsaro: Mun inganta Matakan tsaro a Abuja – ‘Yan sanda

A wani labari kuma, Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa ta kara baza jami’anta a babban birnin tarayya Abuja, bayan rahotannin hare-haren da aka kai wasu sassan birnin.

Rahoton Premium Times Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Legit.NG ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel