Tikitin Jirgin Sama Daga Abuja Zuwa Kano Ya Sake Kaiwa N135,000
- Farashin tikitin sufurin jirgin Sama Daga birnin Abuja Zuwa jihar Kano ya sake haurawa zuwa naira N135,000
- Kamfanonin jiragen sama sun alakantar da tashin farashin tikitin jirgi da tsadar mai da sauran harkokin gudanarwa
- Kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun kara kudin tikiti, inda mafi karanci ya fara daga N80,000, a maimakon N50,000 a baya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja- Farashin sufurin jirgin sama ya kara tashi a Najeriya yayin da fasinjoji ke cigaba da bayyana damurwar su, inda yanzu ake biyan N135,000 daga Abuja zuwa Kano.Rahoton Aminiya Daily Trust
Wannan yanayi yasa mutane da dama na fasa tafiyar su ko kuma su nemi wasu hanyoyin mafi sauki.
Kamfanonin Sufurin jiragen sama dai sun alakantar da tashin gwauron zabon da farashin tikitin jirgin sama yayi ga tsadar mai da sauran harkokin gudanarwa a kamfanonin.
Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima
A shekarar baya, ana sayar litar mai kasa da naira N200, yanzu kuma ya haura N800, kuma ana sa ran zai kai naira N1,000 saboda yaki da ake yi tsakanin kasar Rasha da Ukraine.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsayar da ayyukan kamfanonin jirgin sama na Aero Contractors da Dana da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) yana cikin abun da ya kara tsadar tikitin sufurin jirgin sama a Najeriya.
Bincike ya nuna cewa kusan duka kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun kara kudadensu, inda mafi karanci ya fara daga N80,000, a maimakon N50,000 a baya.
Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden
A wani labari kuma, Shugaba Joe Biden, a jawabin da yayi wa manema labarai a yammacin jiya, ya ce umarnin kai hari da ya ba jiragen yakin Amurka a birnin Kabul na Kasar Afganistan yayi sanadiyar kashe al-Zawahiri.
Al-Zawahiri ya kasance jagora na farko ga tsohon shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden, wanda sojojin Amurka suka kashe a lokacin da yake buya a Pakistan a shekarar 2011.
Asali: Legit.ng