Miyagu Sun Yi Wa Kauye Zobe, Mai ciki Ta Haihu a Hanya, An Yi Gaba da Mutum 50

Miyagu Sun Yi Wa Kauye Zobe, Mai ciki Ta Haihu a Hanya, An Yi Gaba da Mutum 50

  • Wasu ‘yan bindiga sun aukawa kauyen Damari, sun yi nasarar yin garkuwa da mutane barkatai
  • Jawabin Shugaban kungiyar Birnin-Gwari Emirate Progressives’ Union, ya tabbatar da wannan
  • Ishaq Kasai, yace an aukawa garin ne a ranar Asabar, mazauna da dama sun tsere wasu garuruwan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Jaridar Punch ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi barna a wani kauye da ake kira Damari a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Wannan rahoto mara dadi da ya fito a karshen makon da ya wuce, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi sanadiyyar da mutane suke tsere daga Damari.

Ana maganar ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da mutane kimanin 50 da ke zaune a kauyen Damari. Daily Trust ta kawo wannan labari a wani rahoto.

Shugaban kungiyar Birnin-Gwari Emirate Progressives’ Union, Ishaq Kasai, ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar a daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon mummunan hari a Jos

Ishaq Kasai yake cewa a ‘yan kwanakin bayan nan, ana ta kawo masu munanan hare-hare a sanadiyyar tashin ‘Yan kungiyar Ansaru na Boko Haram.

A lokacin da suke nan, Sojojin kungiyar ta’addan na Ansaru sun kasance suna taimakawa wajen hana a kawo hare-hare a kauyukan da ke yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan ta'adda
Wasu 'Yan bindiga a Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kungiyar Birnin-Gwari Emirate Progressives’ Union

“Abin takaicin da ya faru a awanni 72 da suka wuce a garin Damari, mazabar Kazage da ke gabas da Birnin Gwarin jihar Kaduna ya kai intaha.
Zuwa ranar Asabar, ‘yan bindiga suka zagaye Damari, suka yi awon-gaba da kusan mutane 50.
Kafin nan, sojoji daga Dogon-Dawa sun shiga garin, suka raka mazaunan da suka rage da ke da niyyar tserewa wasu makwabta, wasu har Zaria.”

- Ishaq Kasai

Kasai yace mafi ban takaici shi ne wata mai juna biyu da ta tsere tare da mutane da aka bari yayin da ta fadi, ta haifi jariri, amma a karshe duka suka mutu.

Kara karanta wannan

An Ankarar da Jami’an Tsaro Kan Shirin ‘Yan Ta’adda na Kai Hare-Hare a Legas

Damari na cikin mafi girman garuruwan da ke kasar Birnin Gwari, amma a yau akwai mazauna garin kimanin 20, 000 da suka zama ‘yan gudun hijira.

An shiga garin Shika

Ana haka ne kuma muka samu labari cewa ‘yan bindiga sun shiga garin Shika da ke karkashin karamar hukumar Giwa, suka dauke wasu Bayin Allah.

Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana, ‘yan bindigan sun auka wani gida ne a Layin Maje da ke Shika Gari, suka dauke magidanci, matarsa da yaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng