Rarara Ya Shirya Taron Saukar Al-qurani Don Samun Zaman Lafiya A Kasar, Jarumai Maza Da Mata Sun Hallara
- Mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya shirya taron addu'a na musamman don samun ci gaba da zaman lafiya a Najeriya
- Rarara ya tara malamai inda suka yi saukar Al-Qur'ani mai girma tare da yin yanka na rakuma
- Manyan jaruman masana'arta fina-finan Hausa na Kannywood, maza da mata sun hallara a wajen
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Shahararren mawakin nan na siyasa kuma shugaban mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gudanar da wani taron addu’a na musamman.
Rarara wanda ya kuma kasance jagoran tafiyar 13X13 na masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, ya tara malamai inda aka yi saukar Al-Kur’ani domin ci gaban kasar.
Kamar yadda jarumi kuma MC Mallam Ibrahim Sharukan ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce an yanka rakuma biyu bayan addu’an domin tabbatar da zaman lafiyan kasar.
A cikin bidiyon da ya wallafa a shafin nasa mai suna, an gano taron jama’a da Qur’anai a gabansu suna karantawa, sannan kuma manyan jaruman Kannywood maza da mata duk sun hallara a wajen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyoyin a kasa:
Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa
A wani labarin, munkawo a baya cewa Dauda Kahutu Rarara, ya magantu kan gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka.
A cikin wakar, Rarara ya jagoranci wata tawaga ta shahararrun mawakan Hausa karkashin 13X13, wata kungiya ta masana’antar Kannywood.
Lamarin ya haifar da zazzafan martani kan ko babban dan kashenin Buharin baya tare da shi kuma.
Asali: Legit.ng