Bayan Shekaru 27, Dan Najeriya Ya Bazama Neman Malamarsa Ta Firamare, Ya Gano Ta
- Shekaru 27 bayan kammala makarantar firamare, wani dan Najeriya ya bazama neman malamarsa ta aji shida a jihar Neja
- A cewar mutumin mai suna Abdullahi Mohammed Moshood, ya yi nasarar gano malamar tasa mai suna Misis Emily Olowookere
- Ya ce gani na karshe da ya yiwa matar wacce ta koyar da shi a makatar Firamare na Suleiman Barau ya kasance a 1997 amma ta gane shi sarai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abdullahi Mohammed Moshood, wani dan Najeriya mai cike da hikima ya tuna da malamarsa ta aji shida a firamare shekaru 27 bayan ya kammala karatunsa sannan ya yanke shawarar nemanta.
Ya bazama neman matar mai suna Misis Emily Olowookere wacce ta koyar da shi a makarantar firamare na Suleiman Barau, Suleja, jihar Neja.
Moshood ya gano malamarsa
Ga mamakinsa lokacin da ya gano inda take, Misis Olowookere ta gane shi sarai cikin sauki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi kamar bai san matar ba a lokacin da ya gano ta, amma sai ta ce masa shi dalibinta ne kuma ta ambaci sunansa.
Ya rubuta a shafin Facebook:
“Shekaru 27 kenan da kammala karatuna daga makarantar firamare na Suleiman Barau, Suleja, na bazama neman malamata ta aji shida, Misis Emily Olowookere wacce na yiwa ganin karshe a lokacin yaye dalibai a ranar 26 ga watan Yulin 1995. Abun al’ajabi, malamar tawa ta gane ni bayan na yi kamar ban san ta ba.
“Na sha mamaki kuma a gefe guda na yi farin ciki matuka cewa bayan shekaru 27, malamata ta aji shida ta gane ni da sunana. Wannan haduwar farin ciki ne. Shin malamarka Za ta gane ka bayan shekaru 27?”
A wata hira na daban, Moshood wanda ya kammala karatu daga kwalejin fasaha ta Kaduna ya fadama Legit.ng cewa ya yi farin ciki sosai cewa malamar tasa ta gane shi kuma da sunansa daidai. Ya ce ya jinjina mata.
Kalamansa:
“Abun farin cikin shine cewa za ta iya gane ni sannan ta ambaci sunana bayan shekaru 27.”
Jama'a sun yi martani
Olorunfemi Elefin ya ce:
“Dan uwa kada ka damu, facebook za ta taimaka wajen ajiye mana wannan koda kana son zama shugaban kasa sannan suna kokarin fadin shirme. Jinjina gareka da Mama kuma ina godiya da ginshikin da kika maiwa dan uwana.”
Stella Ameh-Iji ta yi martani:
“Lallai ta kasance malama mai tsananin kirki a gareka da har za ka je nemanta. Wannan ba karamin abu bane a gareta kuma ka yi kokari.”
Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici
A wani labarin, wani mutum ya ci ribar aikin al’khairin da ya taba yiwa wani matashi dan makaranta shekaru 15 da suka wuce a 2022.
Ma’aikacin banki dan kasar Ghana, Edward Asare ya bayyana yadda wani mai gyaran takalmi gurgu ya taimaka wajen gyara masa takalmin makarantarsa da ya baci a 2007.
A cewar Asare, yana a hanyarsa ta zuwa makaranta a wata rana kawai sai takalminsa ya lalace.
Asali: Legit.ng