Karin bayani: ASUU ta Tsawaita Yajin Aikinta da Karin Makwanni Hudu
- Yayin da daliban Najeriya ke ci gaba da jiran karshen yajin aikin ASUU, lamurra sun kara dagulewa
- Kungiyar malaman jami'o'i sun bayyana kara wa'adin yajin aikin da suke yi zuwa nan da wata guda
- ASUU ta ba gwamnatin tarayya karin lokaci domin duba ga yarjejejiyar da ke tsakaninsu gabanin samo mafita
FCT, Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kara tsawaita yajin aikin da take da karin wasu makonni hudu domin baiwa gwamnatin tarayya karin lokaci domin biyan bukatun ta.
Kungiyar ta dauki wannan matakin ne a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa a sakatariyar ta ta kasa da ke Abuja ranar Lahadi, The Nation ta ruwaito.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fitar, kungiyar ta ce.
“Bayan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen cika alkawuranta wajen magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2020 (MOA), NEC ta yanke shawarar kare wa'adin yajin aikin zuwa wasu makonni hudu domin baiwa gwamnati karin lokaci don gamsuwa da warware dukkan batutuwan da suka rage.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Yajin aikin zai fara aiki ne daga karfe 12:01 na safe a ranar Litinin, 1 ga Agusta, 2022."
Farin lamarin
Idan baku manta ba, kungiyar ta ASUU ta shafe watanni tana yajin aiki, tun tsakiyar watan Fabrairun 2022 saboda wasu bukatu da gwamnati ta gaza biya musu, rahoton Vanguard.
Ya zuwa yanzu, an sha zaman sulhu tsakanin gwamnati da ASUU, sai dai har yanzu ba a samar da mafita mai daurewa ba.
Dalibai sun yi zanga-zanga a lokuta mabambanta, kana kungiyar kwadago ta hada kai da ASUU a makon jiya domin gudanar da gangamin lumana a fadin kasar nan.
Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU
A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi barazanar korar malaman jami’ar KASU da suka shiga yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa zai kori malaman jami’an jihar Kaduna da suka yi watsi da aikinsu, suka tafi yajin-aiki.
Tun watan Fubrairun shekarar nan kungiyar ASUU ta malaman jami’a take yajin-aiki a kasa, Malaman na zargin gwamnati da kin cika alkawuranta.
Asali: Legit.ng