Matsalar rashin tsaro: Ba a ga komai ba tukuna, malamin addini ga 'yan Najeriya
- Babban malamin addinin kirista ya bayyana yiwuwar samun munanan lamurra nan gaba kadan a Najeriya idan ba a samu mafita ba
- Primate Elijah Ayodele ya hango cewa, cin hanci da rashawa ne suka mamaye kasar nan shi yasa aka gaza samun mafita
- Faston ya yi tsokaci ga abubuwan da ya gani na matsala game da matsalar tsaron kasar nan, kana ya fadi mafita
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Najeriya - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya kara bayyana gargadinsa ga 'yan Najeriya game da matsalar tsaro a Najeriya da ake fuskanta.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya fitar, malamin ya ce har yanzu ‘yan Najeriya ba su ga komai ba kuma matsala na tafe a nan gaba har sai shugaba Buhari ya sauya masu kula da harkokin tsaro a kasar.
Primate Ayodele ya bayyana cewa babban dalilin rashin tsaron Najeriya shine cin hanci da rashawa a tsarin tsaron kasar.
Malamin ya kara da cewa za a kai wa wani gwamna hari tare da yin garkuwa da wasu muhimman mutane a nan gaba kadan, kamar yadda jaridar PM News ta kawo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'an Najeriya za su fara yakar junansu
Idan aka ci gaba a haka, ya bayyana cewa jami’an tsaron Najeriya za su fara yakar juna a kasar nan kuma nan ba da dadewa ba za a yi uwa uba wani gagarumin zanga-zanga na nuna kin jinin faruwar irin wadannan lamurran, inji Daily Post.
Sai dai malamin ya bayyana cewa yanayin tsaron kasar zai iya gyaruwa amma miyagun shugabanni ba sa son ganin karshen matsalar.
Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da ragargazar wasu 'yan ta'adda 30 da ake zargin sun kai hari kan sojojin fadar shugaban kasa a makon nan.
Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja, inda aka hallaka jami'ai uku tare da jikkata wasu.
Daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana aikin da jami'an suka yi a wani taron manema labarai na mako bibbiyu kan ayyukan tsaro a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Daily Nigerian.
Asali: Legit.ng