Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane
- Wata amarya da kawayenta sun sanya mutane tofa albarkacin bakunansu a shafin soshiyal midiya
- Amaryar da kawayenta sun yi shiga ta kamala inda suka rufe koina na jikinsu ruf
- Hakan ya burge mutane da dama inda suka yi fatan dama kowa zai yi koyi da su
Kamar yadda yake kasancewa a tsakanin amare da yan matan amare na wannan zamani, idan aka ce bikin waninsu ya tashi sukan yi shiga ta kece raini.
Hakazalika, wasu kan yi shiga ta nuna tsaraici duk don nuna cewa sun waye da kuma son ganin hankula sun karkata a kansu.
Sai dai wata amarya da kawayenta sun sauya tunani inda suka yi shiga ta kamala a yayin shagalin bikin kawar tasu.
A wani bidiyo da ya yadu a shafin soshiyal midiya, an gano amaryar sanye da doguwar riga irin na amare sannan kanta lullube da mayafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan kawayenta suma sun sanya dogayen rigunan jallabiya fuskokinsu zagaye da mayafi.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Wannan tsari na yadda suka suturta jikin nasu ya burge mutane matuka a shafin Instagram inda suka jinjina masu.
_dark.cofee ta yi martani:
“Wannan ya yi kyau ”
style_avenue_ng
“Ina ma ace kowa zai zama kamar su”
tc_nomy ta yi martani:
“MashaAllah”
i.d.a.r.a.a.a ta ce:
“Duk da cewar ni kirista ce zan so wannan a aurena sun yi kyau matuka”
style_avenue_ng ta ce:
“Shiga ta kamala mashaAllahh”
darling_omaa ta ce:
"Shigar mutunci na da kyau”
nanamira.__ ta ce:
“Masha Allah ”
Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua
A wani labari na daban, an gudanar da shagalin biki na karshe wato ‘budan kan amarya’ Yacine Sheriff wacce aka daura aurenta da angonta Shehu Umaru Yar’adua.
Tun a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli ne aka kulla aure tsakanin dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Muhammad Sheriff amma sai aka ci gaba da shagulgulan biki.
Kamar yadda yake bisa al’adar mutanen yankin arewacin Najeriya a kan rufe taron biki ne da budan wanda dangin ango kan yi bayan an kai amarya gidan mijinta.
Asali: Legit.ng