An Ba Da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci A Jihar Sakkwato

An Ba Da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci A Jihar Sakkwato

  • Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana Ranar Litinin 1 ga watan Agusta 2022 ta zama ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Sakkwato
  • Yau daya ga watan Muharram shekara ta 1444 bayan hijirar Manzon Allah S.A.W Salallahu Alaihi Wasalam
  • Gwamna Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi Addu’a Allah Ya sada mu da rahamarsa da gafara, da kuma yi fatar samun dacewa a cikin sabuwar shekarar Musulunci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Sokoto - Yau daya ga watan Muharram shekara ta 1444 bayan hijirar Manzon Allah S.A.W.

Gwamna Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce bayan tattaunawa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, kan shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci a wannan Jumu’ar kamar yadda Aminiya.Daily Trust ta rawaito.

Tambuwal yace :

“Na ayyana Ranar Litinin 1 ga watan Agusta 2022 ta zama ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati a fadin Jihar Sakkwato.”

Kara karanta wannan

Kiristocin Jagororin APC 4 da Suka Juyawa Tinubu Baya kan Takarar Musulmi-Musulmi

iSLAMIC
An Ba Da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci A Jihar Sakkwato FOTO Legit.NG

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan Tambuwal ya nemi mutane su yi amfani da lokacin hutun wajen bayyana kyawawan dabi’u, kamar yawaita yin sadaka, yin addu’o’in zaman lafiya da samun shugabanci na gari.

Tambuwal yayi kira da a yawaita ayyukan kwarai da bin karantawar adinin musulunci a cikin watannan saboda kasancewar watan a cikin watanni hudu masu daraja da aka hana zub da jini da aikata manyan laifuka

Gwamnan yayi Adu’a Allah Ya sada mu da rahamarsa da gafara, da kuma fatar samun dacewa a cikin sabuwar shekarar Musulunci.

Bidiyon karamar yarinya dake kaunar Sheikh Pantami, ministan ya sha alwashin tuntubar danginta

Bidiyon wata karamar yarinya wacce aka bayyana sunanta da Rukayya dake kaunar Sheikh Ali Isah Pantami ya bayyana.

A wani labari kuma, A bidiyon da 'yar uwar yarinyar mai amfani da sunan @Miss_Luthor ta saki a shafinta na Twitter tare da janyo hankali ministan ta hanyar kiran sunansa, ta sanar da irin kaunar da yarinyar ke wa ministan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel