2023: Kwankwaso Ya Kai Wa Babban Sarkin Arewa Ziyara Don Neman Albarka
Ilorin - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Juma'a ya ziyarci Ilorin, Jihar Kwara don neman albarka daga Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, kan takarar shugabancin kasa, rahoton Leadership.
Farfesa Shuaib AbdulRaheem dan takarar gwamnan Kwara na NNPP da Dr Kolo Baba Jiya, dan takarar sanata na Kwara North da Alh Buba Galadima ne suka yi wa Kwankwaso rakiya zuwa fadar sarkin.
Da ya ke jawabi a fadar sarkin bayan sallar Juma'a tare da Sarkin, Kwankwaso ya ce ya taho ilorin ne domin neman albarka daga sarkin.
Ya kara da cewa ya yi amfani da damar domin bude wasu ofisoshin jam'iyyar NNPP a Ilorin, babban birnin jihar da wasu sassan jihar.
Kwankwason ya kara da cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun taho nan ne domin gaisuwa gare ka a matsayin uban kasa. Muna godiya bisa tarbar da aka yi mana da kuma damar yin sallar Juma'a tare da kai. Na kuma gode wa mutanen jihar bisa karamci da aka mana. Muna addu'a Allah ya bawa sarkin mu tsawon rai da lafiya."
Martanin Mai Martaba Sarkin Ilorin
A bangarensa, Sarkin na Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana Kwankwaso a matsayin 'kwararren dan siyasa kuma shugaba.'
Ya yi addu'a bunkasar tafiyar Kwankwasiyya, ya kara da cewa, "Allah zai cigaba da yi maka jagora. Ina farin cikin yi maka maraba."
Sulu-Gambari ya tabbatarwa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NNPP cewa yana tare da mutum mai karfin fada a ji a jihar, Farfesa Shuaib AbdulRaheem.
Asali: Legit.ng