Kano: Hotunan ragargazajjen asibiti inda mata ke tafiyar 3Km don zuwa haihuwa, ya tada hankalin jama'a
- Hotunan wani asibiti dake yankin Tabanni a cikin jihar Kano ya bayyana kuma abun sai dai a ce Allah ya kyauta
- Mata masu juna biyu suna yin tattakin tafiyar 3 kilomita zuwa asibitin dake gundumar Wagara na karamar hukumar Tofa ta jihar Kano
- A hotunan da aka gani dauke da bayanai, an gano cewa shi ne asibiti daya tilo a yankin, lamarin da yasa jama'a basu da wani zabi sai zuwa nan
Kano - Hotunan mummunan halin da wani asibiti a yankin Tabanni, gundumar Wagara dake karamar hukumar Tofa yake a jihar Kano ya fallasu kuma abun babu kyan gani.
Kamar yadda kungiyar Citizen Advocacy ta wallafa, TrackaNG ta bayyana hotunan a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter inda tace mata masu juna biyu suna tafiyar kilomita 3 domin zuwa haihuwa a ragargazajjen asibitin sakamakon zamansa daya tilo a yankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wallafar:
"Abun mamaki!!! A yankin Tabanni, gundumar Wagara, karamar hukumar Tofa ta jihar Kano, mace mai juna biyu na yin tattakin kilomita 3 domin haihuwa a wannan asibitin.
"Shi ne asibiti daya tilo da ake da shi a yankin kuma yana cikin mummunan yanayi," Trackang ta rubuta.
Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB
A wani labari na daban, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.
Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.
Ya wallafa hotunan kanwar shi a lokacin da wasu suka kawo ta gida da kuma lokacin da ta warware kamar ba ita ba a ranar 27 ga watan Yulin 2022.
"A wannan shaidar, kai tsaye zan je kan maganar abinda zan tattauna a kai, babu dogon labari. Shekaru shida da suka wuce, 'yar uwata ta tashi ta bar gida haka kawai. A cikin wadannan shekarun, na rasa mahaifina da 'yar uwata, mahaifiyata da 'yan uwana suna shan wahala amma mun cigaba da addu'a da yarda da Ubangiji," yace.
Asali: Legit.ng