Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB

Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB

  • Wani mutum ya bayyana yadda kanwarsa ta bar gida ta shiga bariki haka kawai kuma ta kwashe shekaru shida cif
  • Ya bada labarin yadda kanwarsa ta kwaso cutukan kanjamau da TB bayan dadewa da tayi a bariki bata dawo gida ba
  • Kwatsam aka dawo da ita gida magashiyyan, lamarin da yasa suka dage da addu'a har sai da ta tashi kwatsam babu cutukan

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.

Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro Ta Kai Yan Najeriya Bango, NSA Ya Magantu Bayan Taron Yau Da Buhari

Budurwa a bariki
Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB. Hoto daga @soltune
Asali: Twitter

Ya wallafa hotunan kanwar shi a lokacin da wasu suka kawo ta gida da kuma lokacin da ta warware kamar ba ita ba a ranar 27 ga watan Yulin 2022.

"A wannan shaidar, kai tsaye zan je kan maganar abinda zan tattauna a kai, babu dogon labari. Shekaru shida da suka wuce, 'yar uwata ta tashi ta bar gida haka kawai. A cikin wadannan shekarun, na rasa mahaifina da 'yar uwata, mahaifiyata da 'yan uwana suna shan wahala amma mun cigaba da addu'a da yarda da Ubangiji," yace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ana nan tafe, bayan mako daya da aure na samu sakon 'yar uwata cewa wasu sun zo har gida sun ajiye kanwata kamar yadda hoton farko ya nuna.
"Ban yi kuka ba saboda babu wani gurbin nuna ragwanci, na gane cewa ba zan bar wannan haka ba. Sai na tuna wata addu'a ta da nake yi cikin dare. Na cigaba da ihu ina cewa "shaidan, ba za ka samu wannan ba".

Kara karanta wannan

An yi adalci: Mahaifin Hanifa ya yi martani bayan hukunta malamin da ya kashe masa diya

"Na kira wasu daga cikin abokaina, na tura musu hoto kuma nace su yi min addu'a. Na tura wa 'yar uwata kuma nace ta dinga mata addu'ar kowacce safiya.
"Bayan wasu makonni, ta fara tafiya da magana, yayata ta kira ni a wata safiya ta ce " mun je asibiti bayan an duba ta, likita yace TB ya tafi hakazalika Kanjamau din".

Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi

A wani labari na daban, wata budurwa cike da alfahari ta bayyana rawar da iya girkinta ya taka wurin sauya saurayin ta daga siriri zuwa lukuti a hotuna da bidiyo.

A bidiyon da hotunan da @gossipmiltv suka sake wallafawa, budurwar ta nuna yadda suka fara haduwa da saurayin inda yake a siririnsa.

Daga nan ta biyo da hotunan wasu daga cikin girke-girkenta wanda tayi ikirarin take ciyar da saurayin da su.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buhari zai sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

Asali: Legit.ng

Online view pixel