Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi

Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi

  • Wata budurwa ta janyo cece-kuce a soshiyal midiya da tsofaffi da sabbin hotunan saurayin ta da ta wallafa
  • Ta wallafa hotunan inda take nuna yadda yake a baya lokacin da suka hadu da kuma yadda ya canza yayi shar da shi sakamakon iya girkinta
  • Wasu ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani sun zargi budurwar da bashi abinci mai yawa wanda hakan yasa babu budurwar da za ta so shi

Wata budurwa cike da alfahari ta bayyana rawar da iya girkinta ya taka wurin sauya saurayin ta daga siriri zuwa lukuti a hotuna da bidiyo.

A bidiyon da hotunan da @gossipmiltv suka sake wallafawa, budurwar ta nuna yadda suka fara haduwa da saurayin inda yake a siririnsa.

Babe wey sabi
Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi. Hoto daga @gossipmiltv
Asali: Instagram

Daga nan ta biyo da hotunan wasu daga cikin girke-girkenta wanda tayi ikirarin take ciyar da saurayin da su.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Daga nan sai budurwar ta sake saka wani bidiyo inda saurayin ke buga wasan suluka kuma ya bayyana a lukuti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sabon bidiyon, babu shakka ya tara jiki kuma har tumbi ya samu sakamakon dibar gara. Jama'a da dama sun sha mamaki kuma sun yabawa budurwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel