Kotun Musulunci Zata Yanke Wa Abdulmalik Tanko Hukunci Kan Kisan Hanifa a Kano
- A yau ake tsammanin babbar Kotun jihar Kano zata kawo karshen shari'ar kisan Hanifa Abubakar yar shekara 5 a duniya
- Kotun ta sanya ranar 28 ga watan Yuli, 2022 domin yanke wa Abdulmalik Tanko da ake zargi hukunci
- Tun a farkon wannan shekarar ne aka gurfanar da Tanko, shugaban makarantar su Hanifa a gaban Kotu
Kano - A yau Alhamis, 28 ga watan Yuli, 2022 ake sa ran Babbar Kotun Kano zata yanke hukunci na karshe kan shari'ar garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar.
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa ana tuhumar shugaban makarantar da Hanifa ke karatu, Abdulmalik Tanko, da yin garkuwa da yarinyar yar shekara 5, daga bisani kuma ya kashe ta.
Tun a watan Janairu, 2022, Gwamnatin Kano ta gurfanar da Tanko da wasu mutum biyu da ake zargin sun haɗa baki wajen ƙulla sace Hanifa da halaka ta.
Amma daga baya Kotu ta wanke tare da sakin sauran waɗan da ake zargin sun haɗa baki da Tanko, yayin da aka cigaba da tsare shugaban makarantar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda lamarin ya faru tun farko
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa waɗan da ake zargin sun yi awon gaba da Hanifa ne a kan hanyarta ta komawa gida daga Islamiyya, Tanko ya kaita ɗaya daga cikin makarantunsa ya kasheta kuma ya ɓinneta.
Rahotanni bayan ɓatan yarinyar sun nuna cewa a Keke-Napep waɗan da ake zargin suka ɗauki Hanifa kuma iyayenta da sauran su sun yi ta cigiyar inda ta yi amma babu labari har sai bayan kwanaki 46.
Wannan lamari dai ya jawo Alla- Wadai daga mutanen sassan Najeriya, cikinnsu har da mutum lamba ɗaya, shugaban ƙasa Buhari da uwar gidansa, Aisha Buhari, Gwamnan Kano da sauran manyan mutane a Najeriya.
Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari
Da yawan su sun yi kira ga hukumomi su tabbatar doka ta yi aikinta kan waɗan da ake zargi domin kwatar wa marigayya Hanifa haƙƙinta.
Fusatattun mazauna Kano sun babbake makarantar Tanko, kuma yanzu haka kowa na jiran ya ji irin hukuncin da Kotu zata yanke kan wannan ɗanyen aiki.
A wani labarin kuma kun ji cewa Daga kwanciya bacci, Ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ya rasu
A karo na biyu, ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya, Mai shari'a Monica, ya rasu daga kwanciya bacci ranar Asabar.
Bayanai sun tabbatar da cewa marigayin wanda ya karanci lissafi, yana aiki ne da ma'aikatar sufuri ta ƙasa a jihar Legas kamin rasuwarsa.
Asali: Legit.ng