Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU

Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana a game da malaman jami’ar KASU da su ma suke yajin-aiki
  • Mai girma Gwamnan na Kaduna yace Malaman jami’ar jihar Kaduna ba su da dalilin biyewa ASUU
  • El-Rufai ya sha alwashin dakatar da albashin marasa zuwa aji, sannan zai maye gurbinsu da wasu

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi barazanar korar malaman jami’ar KASU da suka shiga yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa zai kori malaman jami’an jihar Kaduna da suka yi watsi da aikinsu, suka tafi yajin-aiki.

Tun watan Fubrairun shekarar nan kungiyar ASUU ta malaman jami’a take yajin-aiki a kasa, Malaman na zargin gwamnati da kin cika alkawuranta.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Da aka yi hira da Gwamnan a gidan rediyo a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli 2022, ya nuna cewa malaman KASU ba gwamnatin tarayya suke yi wa aiki ba.

Mai girma Gwamnan yake cewa ASUU ta na da matsala ne da gwamnatin tarayya don haka bai kamata yajin-aikinsu ya shafi jami’ar jihar Kaduna ba.

El-Rufai: Malaman KASU za su koma aji

“Shugaban jami’a na rikon kwarya ya tabbatar mani da cewa za su koma aiki, kuma na bukaci a bincika ko da gaske sun koma bakin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @govkaduna
Asali: Facebook

Domin da farko na bada umarnin a dakatar da albashinsu. Amma daga baya aka fada mani cewa ba su shiga yajin-aikin ba, sai na ce a bincika.

Duk wadanda suka shiga yajin-aiki, za a bukaci su dawo da albashin da suka karba.”

- Gwamna Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su mamaye Najeriya domin taya ASUU zanga-zangar nuna fushi

Babu aiki, babu albashi

El-Rufai yake cewa ya dauki wannan matakin ne saboda dokar kasa tace babu albashi ga duk wanda bai je aiki ba, don haka ba za a biya masu yaji ba.

“Idan aka cigaba da haka, zan tashi wata rana in sallame su gaba daya, na rantse da Allah. Za mu sallami dukkansu, mu tallata gurabensu a gidajen jaridu.
“Sun taba yin irin haka, sai muka ja-kunnensu, yanzu sun kara maimaitawa. Ina jiran rahoton Kwamishinan ilmi ne kurum. Wallahi za mu sallame su.
Za mu kori duk wadanda suka shiga yajin-aikin nan idan har ba su koma bakin aikinsu ba.”

- Gwamna Nasir El-Rufai

Hutun yin rajistar PVC

A ranar Talata aka samu labari cewa Malam Nasir El-Rufai ya bada hutun kwanaki (daga Laraba zuwa Juma’a) domin mutane su tanadi PVC a jihar Kaduna.

Hutun ya zo daidai lokacin da NLC ta ke zanga-zanga domin nuna goyon baya ga kungiyar ASUU da ta shafe watanni biyar tana yajin-aiki a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng