Jim kadan da Sanatoci suka yi barazanar tsige Buhari, Shugaban kasa ya dauki mataki

Jim kadan da Sanatoci suka yi barazanar tsige Buhari, Shugaban kasa ya dauki mataki

  • Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa domin a tattauna kan batun matsalar tsaro a Najeriya
  • Ba wannan ne karon farko da aka ji Shugaban kasar zai yi zama irin wannan a Aso Rock Villa ba
  • Taron ya biyo bayan barazanar da ‘Yan Majalisar Dattawa suke yi na tunbuke Shugaban Najeriyan

Abuja - Sa’o’i kadan bayan Sanatoci sun yi barazanar tunbuke Muhammadu Buhari daga kan mulki, sai aka ji shugaban kasa ya kira wani taro na gaggawa.

Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya gayyaci shugabannin jami’an tsaro da hafsoshi zuwa taron musamman da za ayi a yau dinnan.

Ana sa rai za ayi wannan zama ne da shugabannin sojoji; hafsun sojojin kasa, Janar Faruk Yahaya, hafsun sojojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Haka zalika akwai hafsun sojojin sama, AVM Isiaka Oladayo Amao, da hafsun tsaro na kasa baki daya, Janar Lucky Irabor da Sufetan ‘Yan Sanda, Usman Baba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

Za ayi wannan zama ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli 2022 a fadar Aso Villa da ke Abuja.

A zaman da majalisar dattawa tayi a jiya, an bijiro da maganar tunbuke Mai girma shugaban kasa muddin gwamnati ta gagara magance matslar tsaro a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Dattawa
'Yan Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Martanin Lai Mohammed

Bayan wannan magana da aka kawo a majalisar, gwamnatin tarayya ta fito ta maida martani.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi magana bayan taron FEC da aka yi a fadar shugaban kasa, yace gwamnati na bakin kokarinta a kan batun.

Alhaji Mohammed ya yabi Sanatocin saboda yadda suka nuna damuwarsu a game da sha’anin tsaro, yace gwamnati na yunkurin ganin an tsare rayuka da dukiyoyi.

Rahoton yace Sanatoci sun yi niyyar a bijiro da muhawara a kan sauke shugaban kasa. Amma shugaban majalisa, Dr. Ahmad Lawan bai bada wannan damar ba.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Matakin da shugaban majalisar dattawan ya dauka ya jawo Sanatocin adawa suka nuna fushinsu karara, suka tattara suka fice daga zauren majalisar kasar a fusace.

Wa'adin Majalisar Dattawa

Sanata Philip Aduda ya fara kawo maganar, yace akwai bukatar Majalisa ta ba shugaban Najeriya wa’adin makonni shida domin ya yi maganin ta’addanci a kasar.

Kamar yadda kuka samu labari, hakan na zuwa ne biyo bayan yawaitar ta'addancin 'yan bindiga da 'yan ta'adda wasu a sassa musamman na Arewacin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng