'Mun gode wa mahaifiyarmu': Tagwaye sun zama matukan jirgi a kamfani, sun ba da sha'awa

'Mun gode wa mahaifiyarmu': Tagwaye sun zama matukan jirgi a kamfani, sun ba da sha'awa

  • ’Yan uwa tagwaye ‘yan kasar Kenya sun kafa tarihi a Amurka bayan samun aiki a kamfanin jirgin sama
  • Tagwayen sun ce burinsu na zama matukan jirgi a lokacin da suke da shekaru uku kacal ya tabbata kuma iyayensu ne suka karfafa musu
  • A cewarsu, ko yaushe suna raka mahaifiyarsu balaguron kasuwanci kuma sukan je filin jirgin sama su dubo mahaifinsu duk ranar Lahadi

Alaska, Amurka - ’Yan uwa tagwaye masu kama daya 'yan kasar Kenya Alex da Alan sun daga tutar Kenya a kasar Amurka, sun faranta ran mutane da yawa a gida.

Alex da Alan sun zama matukan jirgi a kamfanin jiragen sama na Alaska da ke Amurka kuma an yi imanin su ne farkon rukunin matukan jirgi daya da suka kasance tagwaye.

Tagwaye sun fara aiki a kamfanin jirgi, za su fara tashi tare
'Mun gode wa mahaifiyarmu': Tagwaye sun zama matukan jirgi a kamfani, sun ba da sha'awa | Hoto: Alaska Airlines
Asali: Facebook

Kamfanonin jiragen ya ce an dauki Alan aiki ne jim kadan bayan kammala horonsa na sarrafa na'urar kwaikwayo kuma zai kasance a San Francisco, yayin da dan uwansa Alex zai fara tashi daga Los Angeles.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

A cewar kamfanin jirgin, tagwayen sun kaura daga Kenya zuwa California ne sa’ad da suke 'yan shekaru 13 kuma suka zo da matukar kaunar jirgin sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tagwayen suna godiya ga iyayensu saboda daura su kan kaunar jirgin sama. Tun suna 'yan shekara uku, sukan je ganin jirgin sama tare da mahaifinsu a kowace ranar Lahadi bayan ibadar coci.

Mahaifiyarsu ma ta kan kawo su filin jirgin sama yayin da za ta yi tafiyar kasuwanci.

A cewar Alan:

“Bayan na fara wasa da shirin, daga nan shi ke nan. Na san ina kaunar haka [tashi da jirgi] a matsayin sana'a.”

Kamfanin jirgin Alaska shine zabinsu na farko

Kamfanin jirgin Alaska shine zabi na farko ga Alan lokacin da yake neman ci gaba daga kamfanonin jiragen sama na yankin.

Ya ce aiki a kamfani daya da dan uwansa zai ba shi, amma jama’a da al’adun kamfani suka kawo masa tsaiko.

Kara karanta wannan

Runduna ta yi martani kan harin 'yan bindiga suka kai kan jami'an fadar shugaban kasa

Yanzu, su biyun sun ce burinsu shi ne su tashi a jirgi tunda har yanzu ba su samu damar hakan ba saboda sarkakkiyar ayyuka a fagen kamfanin.

Matashi mai shekaru 18 ya ba da labarin yadda ya kera mota daga tarkacen karfe

A wani labarin, wani matashi dan kasar Ghana, Obed Obeng Danso na cibiyar bunkasa al'umma da fasaha ta CONVOTECH da ke garin Tarkwa a yankin yammacin kasar ya kera motarsa ta farko.

Motar ta matashi mai shekaru 18 tana tafiya ne ta hanyar amfani da man fetur ba tare da wani kalubale ba yayin da aka ga tana tafiya ba tare da wani cikas ba a kan titi.

Danso ya shaidawa Ghanaweb cewa a koda yaushe yana mafarkin kera abin hawa, kuma ta hanyar azamar da ya yi, a karshe dai ya tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.