Gwamnatin Oyo Ta Maida Malaman Firamare Da Ta Kora A Baya Kan Aikin Su

Gwamnatin Oyo Ta Maida Malaman Firamare Da Ta Kora A Baya Kan Aikin Su

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da maida malaman Firamare sama da 100 da aka kora ba kan ƙa'ida ba
  • Shugaban hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar, Nureni Adenuran, ya ce Malaman da aka kora daga 2011-2019 ne abun ya shafa
  • Ya yi kira ga ma'aikatan su nunka zummar su a wajen aiki domin saka wa gwamna kan alfarman da ya musu

Oyo - Gwsmnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta maida Malaman Firamare 129 kan aikin su, waɗan da gwamnatin baya ta kora ba bisa ƙa'ida ba, kamar yaddda Premium Times taruwaito.

Shugaban hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar, Nureni Adeniran, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da hadiminsa na midiya, Olamide Adeniji, ya fitar a Ibadan, babban birnin Oyo ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya raba tsabar kuɗi miliyan N172m da abinci ga talakawa 30,436 a karamar hukuma ɗaya

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamnatin Oyo Ta Maida Malaman Firamare Da Ta Kora A Baya Kan Aikin Su Hoto: premiumtimesng
Asali: Facebook

Mista Adeniran ya ce majalisar zartarwan jihar Oyo ta amince da mayar da Malamai 129 da gwamnatin jiha ta kora ba kan ƙa'ida ba tsskanin 2011 zuwa 2019.

Ya ce tuni aka sanar da Malaman kada sun nemi a biya su Albashin tsawon lokacin da basu aiki, wanda gwamnati ta maida shi tamkar sun tafi hutu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adeniran ya yaba wa gwamna Makinde bisa kyaun zuciya da kuma duba ba tare da son kai ba wajen tafiyar da harkokin jihar Oyo, Ledership ta ruwaito.

A cewarsa, wannan maida malaman makarantar da ya yi a baya-bayan nan alama ce ta nasarar da gwamnatinsa ke samu wacce ba zata gogu ba.

Iyalai da dama zasu yi farin ciki -Adeniran

Shugaban hukumar ba da ilimin bai ɗaya na Oyo ya ce:

"Wannan tagomashi ne ga bangaren ilimi. Bayan karin da za'a samu kan ƙarancin Malamai da ake fama da su a makarantun Firamaren gwamnati, dubbannin iyalai da suka shiga kuncin rayuwa saboda dakatar da masu kula da su, zasu gina sabuwar rayuwa."

Kara karanta wannan

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

Saboda haka ya yi kira Malaman su saka wa gwamna Makinde alfarman da ya musuta hanyar zage wa wajen aikin da ya rataya kansu su ninka sadaukarwan su.

A wani labarin kuma Ana batun tsige shi, shugaba Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe uku masu muhimmanci a tarayya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu mutum uku a matsayin shugabannin wasu hukumomin tarayya.

Mutanen da shugaban ya naɗa sun haɗa da Tijjani Ƙaura, Mista Augustine Umahi da kuma Kaftin Junaid Abdullahi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel