Shigar 'yan bindiga Abuja: Jihar Nasarawa ta umarci a rufe dukkan makarantu

Shigar 'yan bindiga Abuja: Jihar Nasarawa ta umarci a rufe dukkan makarantu

  • Gwamnatin jihar Nasarawa ta sanar da rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu saboda ta'azzarar rashin tsaro
  • A makon nan ne 'yan bindiga suka fara kai farmaki wasu yankunan babban birnin tarayya mai makwabtaka da Nasarawa
  • Rahotannin tsaro sun bayyana cewa, akwai yiwuwar samun munanan hare-hare daga tsageru a yankunan kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Nasarawa - Gwamnatin jihar Nasarawa ta ba da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a fadin kananan hukumomi 13 na jihar, a matsayin wani mataki na kare rayukan dalibai.

Hakan ya biyo bayan barazanar tsaro da ake fama da shi a fadin kasar nan, musamman a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

An umarci a rufe makarantu a jihar Nasarawa
Shigar 'yan bindiga Abuja: Jihar Nasarawa ta umarci a rufe dukkan makarantu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An rahoto cewa, tuni gwamnati ta mallaki rahotannin da ke nuni da cewa akwai yuwuwar samun hare-hare a kan al’ummar jihar da ke makwabtaka da babban birnin tarayya Abuja, musamman yankunan Gitata da Umaisha.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

Rufe makarantun na daga cikin kudurin da aka cimma a yayin wani taron majalisar zartarwa na jihar da aka yi, wanda ya gudana a gidan gwamnati da ke Lafia a ranar Laraba, rahoton Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar, kwamishiniyar ilimi ta jihar, Fatu Jimita Sabo, ta ce bayan duba halin da kasar nan ke ciki, gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da bata lokaci ba.

A cewar ta, hakan ya zama wajibi idan aka yi la’akari da kusancin jihar da babban birnin tarayya Abuja da kuma kudurin gwamnati na ganin cewa makarantun Nasarawa, suna gudana cikin yanayi mai kyau.

A bangare guda, ta bayyana cewa wadanda ke azuzuwan karshe na kammala makaraant tuni aka dage jarabawar ta su, musamman a bangaren sakandare.

Kara karanta wannan

Fargabar kai hari fadar Buhari: IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

Gwamnatin Buhari ta yi martani kan barazanar da Sanatocin PDP suka yi na tsige Buhari saboda rashin tsaro

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan barazanar da Sanatocin jam’iyyar PDP suka yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan majalisar suka baiwa shugaban kasar wa’adin makwanni shida domin ya magance matsalar rashin tsaro ko kuma ya fuskanci batun tsige shi.

Da yake magana bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce gwamnatin tarayya tana aiki ba dare ba rana don ganin ta magance matsalolin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel