Yajin Aikin ASUU: Wasu Dalibai Sun Zama Masu Garkuwa Da Mutane, In Ji Shugaban Kungiyar Kwadago, NLC

Yajin Aikin ASUU: Wasu Dalibai Sun Zama Masu Garkuwa Da Mutane, In Ji Shugaban Kungiyar Kwadago, NLC

  • Shugaban hukumar kwadago na kasa, NLC, reshen Jihar Enugu ya ce wasu daliban Najeriya sun zama masu garkuwa da mutane
  • Virginus Nwobodo, ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci mambobin NLC da suka yi zanga-zangan goyon bayan ASUU suka tafi gidan gwamnatin Enugu
  • Nwobodo ya bukaci Gwamna Ifeanyi Uguwanyi ya mika kokensu ga Shugaba Muhammadu Buhari ya duba batun yajin aikin ASUU ya biya musu bukatunsu don yara su koma makaranta

Jihar Enugu - Hukumar Kwadago ta Najeriya, NLC, reshen Jihar Enugu, a ranar Talata ta shiga yajin aikin goyon bayan ASUU da ake yi a kasar.

ASUU da sauran kungiyoyi a bangaren ilimi sun shiga yajin aiki kan rashin amincewa da yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnati.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Yajin Aikin Enugu.
Yajin Aikin ASUU: Wasu Dalibai Sun Zama Masu Garkuwa, Shugaban NLC. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa yajin aikin an fara shi ne na gargadi na mako hudu, ASUU ta cigaba da tsawaita yajin aikin duk lokacin da wa'adin gargadin ya kare.

Masu zanga-zangan, karkashin jagorancin shugaban NLC na jihar, Virginus Nwobodo, sun tafi gidan gwamnatin Jihar Enugu, kuma gwamnan jihar Ifeanyi Uguwanyi da jami'ansa suka tarbe su.

Mr Nwobodo ya fada wa gwamnan cewa sun taho sakatariyar ne domin su roke shi ya mika damuwarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari kan yajin aikin ASUU.

Shugaban kungiyar na kwadagon ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ke watsi da ilimi duk da muhimmancinsa wurin cigaban al'umma, Premium Times ta rahoto.

"Hana yaran mu zuwa makaranta abu ne mai hadari. Wasu daga cikin yaran sun fara garkuwa da mutane. Wasu sun fara aikata laifuka daban-daban," in ji shi.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

"A yanzu da muke magana, yan ASUU suna fushi. An kori mambobinsu da yawa saboda sun kasa biyan kudin gidan haya da sauran kaya."

Wasu daga cikin masu zanga-zangan da suka yi magana a sakateriya sun nuna fushinsu kan rashin bada muhimmanci da gwamnati ke yi don kawo karshen yajin aiki.

Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu kuɗaɗe

A wani rahoton, wani ɗan majalisar dokoki a jihar Kuros Riba, Hilary Bisong, ya tallafawa malaman Jami'ar Kalaba da kuɗi N900,000 don rage radaɗi yayin da yajin aikin ASUU ya ƙi karewa.

Mista Bisong, mamba ne mai wakiltar mazaɓar jiha Boki 2 a majalisar dokokin jihar Kuros Riba, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164