Yan Bindiga, Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Legas, Abuja, Katsina Da Wasu Jihohi 3, In Ji NSCDC

Yan Bindiga, Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Legas, Abuja, Katsina Da Wasu Jihohi 3, In Ji NSCDC

  • Kungiyoyin ta'adda na ISWAP da Boko Haram da yan bindiga na shirin kai hare-hare a Abuja da wasu jihohin Najeriya
  • Hakan na kunshe ne cikin wani takardar sirri da ya fito daga hukumar tsaro ta NSCDC na ankarar da rundunar ta zama cikin shiri
  • A cewar takardar, jihohin da yan ta'addan ke shirin kai hari sun hada da Katsina, Legas, Kaduna, Zamfara, Kogi da FCT Abuja

Hukumar tsaro ta NSCDC ta umurci dukkan rundunonin ta su kasance cikin shiri bayan samun rahoton sirri da ke nuna yan Boko Haram da ISWAP suna shirin kai hari a Abuja da wasu jihohi biyar har da Legas, rahoton Vanguard.

NSCDC.
Katsina, Abuja, Legas Da Wasu Jihohi 3 Da Yan Ta'adda Ke Shirin Kai Hari, NSCDC. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Fargabar kai hari fadar Buhari: IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

Takardar bayanan da ya fito mai dauke da kwanan watan ranar 25 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun mataimakin kwamandan Janar, Dauda Alkali Mungadi, ga rassan rundunar NSCDC ta ce kungiyoyin yan ta'addan sun kammala shirin kai hari Abuja da wasu jihohi.

Takardar ta ce:

"Mun samu sahihin bayanan sirri cewa Boko Haram da ISWAP sun shirya mayakansu da muggan makamai musamman RPG launcher da Bindigu Masu Harbo Jirgin Sama, AA, da Machine Gun, GPMGS, wanda za su kai hari Jihar Katsina.
"A wani bayanin, wasu kungiyoyin yan ta'adda biyu sun shirya kai hare-hare a Arewa maso Yamma, Arewa Ta Tsakiya da Kudu maso Yamma (Katsina, Zamfara, Kaduna, Kogi, FCT da Legas) kamar yadda aka jero.
"Don haka, Kwamanda Janar yana umurtar a tura jami'ai wurare da suka hada da: Makarantu, Wuraren Ibada da Hukumomin Gwamnati a jihohin ku domin dakile yiwuwar hari daga bata garin. A dauki mataki cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Hankulan mutane sun tashi a babban birnin tarayya Abuja da wasu sassan kasar bayan karuwar kai hare-hare ga jami'an tsaro da masu tsaron shugaban kasa a Abuja.

Iyaye Sun Kwashe Yayansu Daga Makaranta A Abuja Bayan Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Da ke Kusa Da

A wani rahoton, kun ji cewa an kwashe dalibai daga makarantar sakandare ta tarayya, FGC, Kwali, Abuja daga dakunan kwanansu bayan harin da yan bindiga suka kai wani gari da ke kusa da makarantar, Daily Trust ta rahoto.

Iyaye sun yi tururuwa zuwa makarantar a ranar Litinin don kwashe yaransu daga makarantar da ke kauyen Sheda, a babban hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wakilin Daily Trust, wanda ya ziyarci makarantar a ranar Litinin ya ce ya ga wasu iyaye suna kwashe yaransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164