Hotunan Yadda Dan Siyasar Kebbi Ya Zage Yana Taya Al’ummar Mazabarsa Sharan Kwata
- Yan siyasan Najeriya sun iya kirkiro dabaru iri-iri idan aka ce lokacin zabe ya tsaya kuma za su nemi kuri'un talakawa
- Hotunan wani dan siyasar jihar Kebbi sun karade shafukan soshiyal midiya inda aka gano shi yana sharewa al'ummar mazabarsa kwata
- Lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai, yayin da wasu suka ce duk wannan abu da yake yi don samun kuri'u ne
Kebbi - Kamar yadda yake bisa al’adar yan siyasar Najeriya, a duk lokacin da aka ce guguwar zabe ta kado, sai su dunga dagewa wajen yin abubuwan ban mamaki.
A irin wannan lokacin ne za a ga sun kusanci talakawansu sosai harda su dunga shiga sabgarsu wajen aiwatar da wasu ayyuka da karfinsu.
Hakan ce ta kasance a bangaren wani dan siyasa a jihar Kebbi, inda aka gano hotunansa yana taya al’ummar mazabarsa sharan kwata.
Tuni hotunan dan siyasan cikin kyakkyawan shiga ta shadda da hula zanar bukar yana share kwata suka karade shafukan soshiyal midiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan lamari ya sanya yan Najeriya cikin al’ajabi yayin da wasu ke tambayar dalilinsa na yin irin wannan shiga harda hula da agogon hannu alhalin yana aikin share kwata.
Kalli hotunan wanda shafin LIB ya wallafa a kasa:
Jama’a sun yi martani
officialmichaelngene ta yi martani:
"Dukka wannan don kuri’u ne "
julietsisqo ta ce:
"Wadannan mutanen sun zata bamu da tunani ne"
vic_ageless ta ce:
“Wato ya yi iyo a cikin dattin yayin da yake sanye da shiga ta kamala…yallabai a nemi wata dabarar ”
_tbosslane_ ta ce:
“Yallabai idan ka gama hoton ka ajiye abun da ke hannunka sannan ka fito daga wajen Nosa."
APC Ta Sha Kaye Yayin Wani Kayataccen Gasa Da Aka Yi Wajen Wani Bikin Aure, Labour Party Ta Haye
A wani labarin, Najeriya ta yi kaurin suna wajen hada kayataccen liyafar aure musamman ma idan aka yi dacen haduwa da mai gabatar da shiri wato MC wanda ya san kan aikinsa, harma da kirkiran gasa tsakanin amarya da ango.
Wani MC ya kawo sabon salo a wajen wani bikin aure inda ya gabatar da wani gasa wanda ya birge mutane a shafukan soshiyal midiya.
An yi gasar ne tsakanin amarya da ango inda suka rike kwalaye daban-daban rubuce da sunayen jam’iyyun siyasa yayin da wasu mahalarta taron za su yi rawa a bayansu don nuna wanda suke goyon baya.
Asali: Legit.ng