Gwamnati Ta Fara Ƙidayar Karuwai Da Ke Zaune a Jihar Bauchi

Gwamnati Ta Fara Ƙidayar Karuwai Da Ke Zaune a Jihar Bauchi

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta fara kidayar karuwai da ke zauna a jihar inji kwamishinan Hisbah Aminu Balarabe
  • Balarabe ya ce an fara shirin ne da nufin tallafawa karuwan da jari su, koyar da sana'o'i da kuma daukan nauyin masu son aure
  • Hafsat Aliyu da ta yi magana a madadin karuwan ta ce a shirye take ta dena domin kama sana'a da zai bata ikon bada gudunmawa a jihar

Bauchi, Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta fara wani aikin kidaya na mako daya domin sanin adadin karuwai da ke zaune a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan dindindin, Hukumar Hisban na jihar Bauchi, Aminu Balarabe, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da kidayar karuwan, a ranar Laraba a jihar Bauchi.

Gwamnati Ta Fara Ƙidayar Karuwai Da Ke Zaune a Jihar Bauchi
Taswirar Jihar Bauchi. Hoto: The Punch
Asali: UGC

A cewar PM News, Balarabe ya ce an tsara shirin ne da niyar tallafawa karuwan da kudade don su dena karuwanci, su koyi sana'o'i su zama masu dogaro da kansu.

Kara karanta wannan

Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

Ya ce gwamnatin jihar za ta taimakawa karuwan da ke son a sada su da yan uwansu, ya kara da cewa ba don cin mutuncinsu ko nuna wariya yasa aka bullo da shirin ba.

A cewarsa, kidayar, za ta taimakawa gwamnatin jihar ta yi shiri sosai ta kuma gano irin kudi da wasu abubuwan da ake bukata domin taimakawa karuwan su canja rayuwa.

Ya ce:

"Gwamnatin jihar ta na son taimaka musu da jari da koyar da su sana'o'i domin su dena karuwanci.
"Wadanda ba yan jihar Bauchi bane za mu sada su da iyalansu idan suna so. Gwamnati za ta tuntubi gwamnatocin jihohinsu ta yi tsare-tsaren da suka dace don mika su."
"Za mu raba wa karuwan takarda don samun bayanai a kansu kamar jihohinsu na asali da dalilin da yasa suka fara karuwanci.
"Za kuma su zabi irin sana'ar da suke sha'awa. Gwamnati za ta dauki nauyin auren wadanda ke da niyyar yin aure ko sake aure.

Kara karanta wannan

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

"A shirye muke mu aiwatar da tanade-tanaden shari'a kamar yadda dokar jihar mu ta ce amma kuma za mu yi la'akari da hakkin kowa a matsayinsa na dan adam."

Martanin karuwai bisa kidayar da gwamnatin ta fara

Hafsat Aliyu, wacce ta yi magana a madadin karuwan ta bukaci gwamnatin ta cika alkawarin da ta dauka na tallafawa karuwan da suka shiga shirin.

Hafsat ta bayyana niyyarta na dena karuwanci ta kuma fara sana'a da zai taimakawa zamantakewa da tattalin arzikin jihar.

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

A wani labarin daban, kun ji cewa manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

Kara karanta wannan

Ku Kawo Nnamdi Kanu Kotu Idan Ba Kashe Shi Kuka Yi Ba, IPOB Ta Faɗa Wa DSS

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: