'Yan bindiga sun kashe mutum uku, sun sace shugaban jami'an tsaro a Jalingo

'Yan bindiga sun kashe mutum uku, sun sace shugaban jami'an tsaro a Jalingo

  • Mazuana wasu yankuna a babban birnin jihar Taraba na rayuwa cikin tsoro da fargabar harin yan bindiga
  • Wasu tsagerun yan ta'addan sun farmaki birnin da tsakar daren Litinin, inda suka kashe mutane suka sace shugaban Yan sa'kai
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun sace wasu yan mata biyar a harin bayan kashe mutum uku

Jalingo, jihar Taraba - Tashin hankali da tsoro ya mamaye zuƙatan mazauna Jalingo, babban birnin jihar Taraba yayin da ƙarar harbe-harbe ya karaɗe birnin lokacin da yan bindiga suka kai hari da tsakar daren Litinin.

'Yan bindigan, a rahoton da Daily Trust ta tattara, sun kashe mutum uku kuma suka yi awon gaba da shugaban dakarun tsaron Bijilanti na garin da wasu ƴan mata biyar.

Kara karanta wannan

An bayyana sunaye da cikakken bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe a Abuja

Lamarin ya auku ne ranar Asabar da kuma tsakar daren ranar Litinin a wurare daban-daban cikin kwaryar birnin Jalingo.

Taswirar jihar Taraba.
'Yan bindiga sun kashe mutum uku, sun sace shugaban jami'an tsaro a Jalingo Hoto: channelstv
Asali: UGC

Wani rahoto ya bayyana cewa wani mazauni mutum ɗaya da kuma jami'in hukumar yan sanda ɗaya sun rasa rayuwarsu a harin dare a yankunan Lasandi, BabaYau da Sabongari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan kuma, yan bindiga sun sace shugaban yan Bijilanti mai suna Bashir da wasu mata biyar da misalin karfe 1:30 na tsakar dare a Saminaka Junction ranar Litinin.

Bayanai sun tabbatar da cewa maharan kan Babura sun shiga yankin suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su tilasta shiga gidan shugaban Yan Bijilanti.

Da farko yan bindigan sun gamu da tirjiya daga jami'an tsaro amma suka ci ƙarfin su, daga bisani suka tasa shugaban yan Sa'kai da kuma ƴan mata guda biyar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron Villa, sun kashe 8 bayan barazanar sace Buhari

Bincike ya nuna cewa yankin da abun ya faru na kan hanyar zuwa sansanin yan bindiga da ke Dajin Kwando a karamar hukumar Ardo-Kola, a jihar Taraba.

Sama da mutum 20 aka yi garkuwa da su, wasu mutum huɗu ciki har shugaban ƙaramar hukumar Ardo-Kola suka rasa rayukansu a hannun yan bindiga a yankin cikin yan watannin da suka gabata.

Bamu iya bacci da ido biyu yanzu - Mazauna

Mazauna yankin da aka zanta da su sun bayyana cewa yanzun suna rayuwa ne cikin tsoro saboda yawaitar hare-haren yan bindiga.

Ɗaya daga cikin mazauna, Musa Garba. ya ce, "Ina bacci da ido ɗaya a buɗe saboda ba bu wanda ya san wace Anguwa ko gida yan bindigan zasu kai hari na gaba ba."

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ba'a same shi ba bare ya yi tsokaci kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ma'aikatar ilimi ta ba da umarnin garkame makarantun gwamnatin tarayya na Abuja

A wani labarin kuma kun ji cewa Yan bindiga sun yi wa sojoji kwantan ɓauna, sun buɗe musu wuta a Abuja

Miyagun yan bindiga sun farmaki tawagar dakarun sojoji da ke aikin sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari a birnin Abuja.

Wasu bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa yan ta'adda na kewaye da yankin da nufin kai farmaki, inji wata majiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262