An bayyana sunaye da bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe
- A jiya Litinin ne wasu yan ta'adda suka mamayi dakarun soji da ke tsaron fadar shugaban ƙasa a yankin Bwari a Abuja
- Harin ya yi sanadin mutuwar jami'ai guda uku, cikakken bayanan wasu daga cikin mamatan sun bayyana mun tattara muku su
- Wasu bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa yan ta'adda na shirin kai hari makarantar lauyoyi da ke yankin
Abuja - Bayanan wasu daga cikin jami'an da suka rasa rayukan su lokacin da yan ta'adda suka musu kwantan ɓauna a birnin tarayya Abuja ya bayyana.
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda Kaftin ɗin soja da wasu sojoji biyu suka mutu sanadin harin yan ta'adda a yankin Bwari a FCT Abuja ranar Lahadi da daddare.
Mamatan jami'an, waɗan da ke tare da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa, an mamaye su ne ba zato yayin da suke kan hanyar zuwa makarantar Lauyoyi da ke Bwari bayan samun kiran gaggawa daga hukumar makarantar.
Hukumar makarantar ta ankarar da dakarun sojin cewa yan ta'adda sun aike da wata wasika da ke nuna suna gab da kai hari makarantar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin dakarun tsaron, Godfrey Anebi Abakpa, ya tabbatar da kai harin, amma ya ce sojoji sun mamaye cikin dazuka domin tabbatar da ba wasu yan ta'adda da suka fake a ciki.
Sojojin da suka rasa rayuwarsu
Bayanai sun nuna cewa Laftanar Ibrahim Suleiman, da Kaftin Samuel Attah, waɗan da yan asalin jihar Kogi ne, sun rasa rayuwarsu yayin harin na kwantan ɓauna.
Suleiman, ɗa ne ga Kanal Suleiman Ahmodu Babanawa (mai ritaya) kuma ɗan asalin garin Okpo ne da ke ƙaramar hukumar Olamaboro. Marigayi Attah ya fito ne daga ƙaramar hukumar Ibaji duk a jihar Kogi.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tuni mutane suka fara tura sakon ta'aziyya ga iyalan mazajen sojojin da suka rasa rayuwarsu.
Haka zalika yan ta'aziyya sun yi tururuwa a gidan Kanal Babanawa mai ritaya da ke garin Okpo, ƙaramar hukumar Olamabaro domin jajanta masa rashin ɗansa.
A wani labarin kuma Fasinjan Jirgin ƙasan Kaduna da ya kubuta ya magantu kan Bidiyon dukan Fasinjoji
Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka samu kubuta jiya ya ce yana tausaya ragowar da ke hannun yan ta'adda.
Hassan Usman, wanda ya kasance lauya, ya bayyana yadda rayuwarsu ta kasance a sansanin yan ta'adda.
Asali: Legit.ng