Babban Masallaci, Sauran Wuraren da Boko Haram ke Shirin Kai wa Hari a birnin Abuja
- ‘Yan ta’addan Boko Haram da ‘Yan bindiga sun tare a wasu unguwanni a Babban birnin tarayya
- Miyagun su na kokarin kai hari a wasu makarantu da wuraren da Bayin Allah suke yin ibada
- A halin yanzu wasu mazaunan Abuja su na rayuwa cikin dar-dar, bayan bayyanar ‘yan ta’addan
Abuja - Babban birnin tarayyar Najeriya na Abuja na fuskantar barazanar tsaro a halin yanzu, ‘yan ta’adda na shirin kai wasu munanan hare-hare.
Rahoto na musamman da Daily Nigerian ta fitar a ranar Talata, 26 ga watan Yuli 2022 ya nuna ISWAP, Boko Haram da ‘yan bindiga su na shirya ta’adi.
Miyagun za suyi yunkurin aukawa makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari, sannan za su iya kai hare-hare a wuraren da ake ibada a Abuja.
Jaridar ta ce bayanin da aka samu ya nuna ‘yan ta’addan za su iya aukawa wurin aikin jami’an tsaro.
Wannan ya biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali da ke Kuje, suka yi nasarar kubutar da mutane sama da 600 da aka garkame.
Gungun Kachalla Ali Kawaje
Wata majiya ta shaidawa jaridar yaran Kachalla Ali Kawaje da Kachalla Dansadi suna neman yadda za su sace mutane daga makarantar lauyoyin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami’an tsaro sun samu labari ‘Yan bindigan na kokarin shiga makarantar koyon aikin shari’an da nufin garkuwa da dalibai, malamai da ma’aikata.
Kawaje da mayakansa sun gagara a dajin Kuyambana da ya ratsa Zamfara, Kebbi, Kaduna da Neja. Yaransa ne suka harbo jirgin saman sojoji kwanaki.
'Yan ta'adda sun gama lalube
Idan sun samu yadda suke so, ‘yan ta’addan da ‘yan bindiga za su dasa bam da sauran miyagun makamai, tuni sun gama sintirin da za su yi a inda suka fake.
Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron Villa, sun kashe 8 bayan barazanar sace Buhari
Babban masallacin birnin tarayya Abuja yana cikin wuraren da Boko Haram da Ansaru suke hari. ‘Yan ta’addan sun fara hada-kai da wasu 'yan garin.
Hankalin mutane dai ya tashi a garuruwa kamar su Kawu, Bwari bayan an hangi wasu ‘yan ta’addan suna yawo a Gidan Mallam da ke iyaka da dajin Rinji.
Tir da Shugaba Buhari
Dazu aka ji masu bibiyar Facebook sun ce ana kokawa kan ta’adin ‘Yan bindiga, amma Muhammadu Buhari yana maganar gasar wasannin Duniya.
Ana tsakiyar Allah-wadai da cin zarafin fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna da aka sace, sai kuma aka ji labari Muhammadu Buhari zai shilla kasar Laberiya.
Asali: Legit.ng