Baba ya cinye taro: Bidiyon Obasanjo mai shekaru 85 yana kwasar rawa cike da farin ciki ya kayatar
- Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, a cikin kwanakin nan ya janyo cece-kuce bayan fitar bidiyonsa a wani taro
- A bidiyon da ke tashe, an ga tsohon mai shekaru 85 yana rawa tare da girgijewa cike da farin ciki yayin da Sunny Ade ke rera waka
- Shugaban kasan da ya tsufa, babu shakka ya cinye wurin domin ya dishe tauraruwar mutane inda aka taru ana kallonsa tare da masa manni
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya tausasa zukatan ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani bayan bidiyonsa yana rawa ya bazu.
Tsohon shugaban kasan yana daga cikin baki na musamman da Gimbiya Dakta Folashade Omotade ta gayyata wurin liyafar nadin sarauta da aka yi mata.
A bidiyon da City People suka wallafa a shafinsu na Instagram, tsohon shugaban kasan mai shekaru 85 ya bayyana ya warwasawa yayin da mawaki King Sunny Ade yake ta kwarzanta shi da kalamai masu dadi a cikin waka.
Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini
Obasanjo ya fara da rungume mawakin bayan ya fito filin rawan sannan ya fara takawa cike da farin ciki yayin da bakin da ya birge suka cigaba da kallonsa da murmushi cike da fuskokinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wasu bakin sun kara ingiza Obasanjo ta yadda suka dinga masa watsi da kudi yayin da ya cigaba da rawansa.
Mai taro mai gayya ta bai wa tsohon shugaban kasan fili domin ya wataya kuma ta sanar da mutane cewa su bashi filin ba tare da an katse masa hanzarinsa ba.
Ai kuwa hakan yasa tsohon shugaban kasan ya nuna wa jama'a shekaru ba komai bane inda ya dinga tikar rawarsa yana sama, yana kasa tare da kaiwa hagu zuwa dama.
Ga bidiyon mai matukar kayatarwa:
Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a
A wani labari na daban, a wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta da kafafen sadarwa da ke kan yanar gizo, an ga tsohon shugaban kasar Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa tare da wasu mutane.
Bidiyon ya yi matukar farin jini tare da bawa mutane mamakin ganin tsohon shugaban kasa mai yawan shekaru kamar na Obasanjo amma yana iya motsa jikinsa haka.
Tsohon shugaba Obasanjo ya mulki Nigeria a matsayin soja kafin daga bisani ya sake samun mulki a matsayin farar hula.
Asali: Legit.ng