Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a

Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a

- Tsohon shugaban kasar Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya na daga cikin tsofin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da har yanzu ake jin duriyarsu

- Obasanjo ya shugabanci Nigeria a mulkin soji da farar hula

- Duk da yawan shekarunsa da kuma takurkushewar sa'o'insa, har yanzu Obasanjo ya na da koshin lafiya

A wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta da kafafen sadarwa da ke kan yanar gizo, an ga tsohon shugaban kasar Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa tare da wasu mutane.

Bidiyon ya yi matukar farin jini tare da bawa mutane mamakin ganin tsohon shugaban kasa mai yawan shekaru kamar na Obasanjo amma yana iya motsa jikinsa haka.

Tsohon shugaba Obasanjo ya mulki Nigeria a matsayin soja kafin daga bisani ya sake samun mulki a matsayin farar hula.

KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

A makon da ya gabata ne Obasanjo ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi aiki tukuru tare da yin addu'a domin samun nasarar ƙasar nan a sabuwar shekara mai kamawa, kamar yadda today.ng ta rawaito.

Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a
Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a
Asali: Facebook

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Obasanjo ya nuna ƙin amincewarsa cewa Allah ne ya ƙaddara halin talauci da Najeriya ke ciki, inda ya dora alhakin hakan ga shugabannin da suka jefa ta cikin wannan mayuwacin halin.

A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel