Tashin Hankali, Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Ɓauna a Abuja

Tashin Hankali, Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Ɓauna a Abuja

  • Miyagun yan bindiga sun farmaki tawagar dakarun sojoji da ke aikin sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari a birnin Abuja
  • Wasu bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa yan ta'adda na kewaye da yankin da nufin kai farmaki, inji wata majiya
  • A cewarsa, harin da aka kai wa sojojin, wanda mutum uku suka jikkata ya tabbatar da akwai ƴan ta'adda a yankin

Abuja - Sojoji uku sun jikkata yayin da wasu tsagerun yan ta'adda suka farmaki dakarun da ke Sintiri a kan hanyar Kubwa-Bwari, a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Wasu bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa yan ta'adda sun kewaye Abuja da nufin kai hari makarantar lauyoyi da ke Bwari da sauran gine-ginen gwamnati.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ma'aikatar ilimi ta ba da umarnin garkame makarantun gwamnatin tarayya na Abuja

Wata majiya daga hukumar soji da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce harin da aka kai wa Sojojin ya tabbatar da cewa yan ta'adda sun kewaye birnin amma hukumomi sun ce suna ɗaukar mataki.

Sojoji.
Tashin Hankali, Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Ɓauna a Abuja Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar wata majiya, Dakarun sojin Bataliya ta 7 na kan aikin Sintiri a hanyar Bwari-Kubwa, yan ta'adda suka musu kwantan ɓauna suka buɗe musu wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa sojoji uku sun samu raunuka yayin gwabzawa kuma tuni akai gaggawar ɗauke su zuwa Asibiti domin ba su kulawa.

"Harin kwantan ɓaunan da ya faru a cikin yankin Bwari ya nuna cewa 'yan ta'adda na cikin yankin kuma da yuwuwar su kaddamar da hari kan makarantar lauyoyi kamar yadda bayanai suka tabbatar," inji majiyar.

Sojoji sun dakile harin cikin nasara - Kakaki

Da aka tuntuɓe shi, mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar masu ba da tsaro, Kaftin Godfrey Abakpa, ya tabbatar da cewa an farmaki sojoji amma sun yi nasarar daƙile harin.

Kara karanta wannan

Bidiyon azabtarwa: Iyalan Fasinjojin jirgin ƙasa sun mamaye ma'aikatar Sufuri a Abuja, sun hana kowa shiga, Hotuna

Yace:

"An kai musu hari amma an samu nasarar dakile harin. Wasu dakarun sun ji raunuka kuma tuni aka kai su asibiti don ba su kulawa. A halin yanzun dakarun mu sun bazama don magance yan ta'adda da ke barazana a yankin."
"Muna shawartan mazauna su cigaba da harkokin su na yau da kullum yadda suka saba kuma su cigaba da bamu haɗin kai ta hanyar bamu bayanan sirri da zasu taimaka wajen yaƙar bara gurbi."

A wani labarin kuma kun ji cewa Daga kwanciya bacci, Ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ya rasu

A karo na biyu, ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya, Mai shari'a Monica, ya rasu daga kwanciya bacci ranar Asabar.

Bayanai sun tabbatar da cewa marigayin wanda ya karanci lissafi, yana aiki ne da ma'aikatar sufuri ta ƙasa a jihar Legas kamin rasuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262