‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata
- Wani bidiyo na ‘ya da uwa cike da shauki da tunanin barin junansu a wajen liyafar bikin diyar ya bayyana a shafin soshiyal midiya
- A cikin bidiyon, an gano amaryar rungume da mahaifiyarta suna zubar da hawaye na kewar juna yayin da ake gab da mikata gidan miji
- Wannan lamari ya taba zukatan mutane inda aka shawarci ango da ya yi kokari ya rike wannan amanah da za a bashi
Hausawa kan ce aure shine babban yakin mata domin za su bar iyaye, yan uwa da danginsu sannan su koma rayuwa cikin wasu sabbin mutane da basu sani ba.
Wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya na wata amarya da ta fashe da kuka a wajen liyafar bikinta.
A cikin bidiyon wanda shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano amaryar tsaye rike da hannayen mahaifiyarta a filin rawa inda mai gabatar da shirin ta bukaci da ta fadawa mahaifiyarta tana kaunarta kuma za ta yi kewanta.
Yanzu Haka Gwamnati Zata Zuba Ido Tana Kallo, Ali Nuhu Ya Yi Martani Kan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa
Da furta kalmar kewa, sai amaryar ta rungume mahaifiyar tata inda suka fashe da kuka su dukka biyun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano amaryar tana share hawayenta da na mahaifiyarta inda mai kida ya saka masu wakar ‘Wayyo Allah mamana’ na Ali Jita.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama' sun yi martani
Daya daga cikin mabiya shafin sabah_collections ta roki angon a kan ya yi hakuri ya rike wannan amana
ta ce:
"ango a riqe amana "
clyymaxxheritagetravels ta ce:
"Abun ya yi kyau"
Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu
A gefe guda, kawo cewa diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Fatima Kashim Shettima na shirin shiga daga ciki.
Za a dai kulla auratayya a tsakanin Fatima da masoyinta Sadiq Ibrahim Bunu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.
Bidiyon magidanci da kanwar matarsa a bandaki, yayi alkawarin siya mata iPhone idan ta kwanta da shi
Sai dai kuma kamar yadda aka saba bisa al’adan bikin ‘ya’yan manya a Najeriya, tun a makon nan ne aka fara gudanar da shagulgulan bikin.
Asali: Legit.ng