Babu Makawa Sai Mun Tarwatsa Najeriya, In Ji Dan Ta'addan Da Ya Tsere Daga Kuje

Babu Makawa Sai Mun Tarwatsa Najeriya, In Ji Dan Ta'addan Da Ya Tsere Daga Kuje

  • Daya cikin yan ta'addan da suke rike da fasinjojin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja ya yi barazanar cewa za su tarwatsa Najeriya
  • Dan ta'addan wanda ya yi ikirarin cewa yana daga cikin wadanda suke tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja ya ce yana neman Shugaba Buhari da El-Rufai don ya kashe su
  • Yan ta'addan sun ce su aikin Allah suke yi kuma sun yi imanin cewa Allah yana tare da su kuma ba za su fara ba sai sun cimma nasarar tarwatsa kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Daya cikin yan ta'addan da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja yayin harin da aka kai a ranar 5 ga watan Yulin 2022 ya yi barazanar tarwatsa Najeriya, rahoton Daily Trust.

Daily Trust ta rahoto yadda wadanda suka sace fasinjojin jirgin suka yi murna bayan ISWAP ta kai hari a Kuje ta saki fursunoni fiye da 800 ciki har da yan ta'adda da ke tsare.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka Gwamnati Zata Zuba Ido Tana Kallo, Ali Nuhu Ya Yi Martani Kan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Harin Gidan Yarin Kuje.
Babu Makawa Sai Mun Tarwatsa Najeriya, In Ji Dan Ta'addan Da Ya Tsere Daga Kuje. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Yan ta'adda, tunda farko sun bukaci a saki wasu yaransu da kwamandojinsu a matsayin sharadi na sakin wasu fasinjojin.

Sun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya amma tun bayan harin gidan yarin, tattaunawar ta dauki sabon salo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bidiyo mai tada hankali da yan ta'addan suka fitar, an ga wani fursuna da ya ce ya tsere daga Kuje sanye da kayan sojoji da bindiga da harsashi.

Ya bayyana wadanda aka sace din a matsayin 'datti' da aka so yin amfani da su don samun yancinsa.

Da ya ke magana ga shugaban kasa, ya ce:

"Dole sai mun tarwatsa kasar, idan kana so ka bi addinin gaskiya, ka zo ka yi hakan amma ba za mu fasa ba. Ka sani dole za mu kamo ka kuma mu kawo ka daji mu yanka ka tare da El-Rufai. Ka kalle ni, kun aika hotuna na ko ina domin mutane su kama ni amma nima ina sanarwa duk wanda ya gan ku (Buhari da El-Rufai) ya kawo min ku, don in kashe."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Saki Sabon Bidiyo Yadda Suke Azabtarda Fasinjojin Jirgin Ƙasa, Sun Faɗi Shirin Su

Wani dan ta'addan ya yi ikirarin cewa yana samun taimako daga kasahen waje don haka gwamnatin Najeriya ba za ta iya taka musu birki ba.

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun Sace Mutune 50 A Jihar Neja

A wani rahoton, yan ta'adda sun sace mutane hamsin daga garin Kuchi, a karamar hukumar Munya na Jihar Neja, The Punch ta rahoto.

A cewar shugaban kungiyar matasan Shiroro a Jihar Neja, Sani Kokki, wanda ya bayyana hakan cikin sanarwar da ta bawa The Punch, ya ce an sace mutanen ne misalin karfe 2 na dare yayin da ake ruwan sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164