Duk matar da ba ta farkawa kafin karfe 8 a gidan namiji to malalaciya ce, wani ya tada kura a intanet

Duk matar da ba ta farkawa kafin karfe 8 a gidan namiji to malalaciya ce, wani ya tada kura a intanet

  • Wani mai amfani da shafin sada zumunta ya bayyana ra'ayinsa a kan matan da suke shantakewa a gado har karfe 8 na safe a gidan abokin zama
  • @jon_d_doe ya bayyana cewa sai dai idan matar ba ta da lafiya, amma rashin tashi bacci da wuri alama ce ta lalaci ko rashin sha'awar namijin
  • Daga nan ne maganarsa ta karade kafafen sada zumunta, kuma ta haifar da cece-kuce daga mutane da dama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani mai amfani da shafinsada zumunta ya fadi ra'ayinsa game da matan da suke kwanciya dirsham a gidan saurayi maimakon tashi da wuri su shagaltu da lamurran gida.

Mutumin mai suna @jon_d_doe a Twitter ya rubuta wani sakon da ya jawo cece-kuce akan manhajar wacce ta yi kauri wajen samun mutanen da ke wasu a gaba kan ra'ayoyinsu.

Kara karanta wannan

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

Duk mace mai kwanciyar dirsham har 8 bata cancanta ba
Duk matar da ba ta farkawa kafin karfe 8 a gidan miji to malalaciya ce, wani ya tada kura a intanet | Hoto: Stock Image/GettyImages
Asali: UGC

A cewar @jon_d_doe:

“Idan budurwarka ta zo cin hutun karshen mako tare da kai, kuma ta kwanta har zuwa karfe 8 na safe, hakan na iya zama alamar cewa malalaciya ce ko kuma ta raina ka. Sai dai in bata da lafiya. Za ku fahimci wannan rubutun lokacin da kuka yi aure kuma ku fara haihuwa. Karshe kena."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Twitter sun yi martani

Jama'ar shafin twitter da suka ga rubutun sun yi martani kan wannan batu. Yayin da wasu suka amsa da tsantsar zolaya da shagube, wasu kuma sun samu rabuwar kai; wasu suka amince da batun, wasu kuma suka zo da tsalle.

@PabloHoggs ya ce:

“Yarinya mai hankali da tarbiyya za ta san cewa bai kamata ta kasance a kan gado ba (a gidan saurayi) a lokacin. Tsaftace gidan da nuna kwarewar ki a madafa ya kamata ya zama abu na farko. Wannan kawai na kara sa maza su kamu da soyayya."

Kara karanta wannan

Kannywood: Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce

@iampreciousben ya rubuta

“Abin ban dariya ne irin abubuwan da maza ke amfani da su don gwada mata. Na taba ziyartar wani saurayi kuma na kasa shiga bandakinsa saboda datti ainun kuma ina bukatar wanka da yin fitsari don haka sai da na wanke bandakin don in yi amfani da shi. Dakin ma dai gashi nan kaca-kaca, karkashin gadonsa kamar motar lawma.”

@DanielRegha ta yi sharhi:

“Ya kamata macen da ta kwana a gidan namiji ta farka da karfe 7 na safe don ta taimaka wajen gyara gidan, amma idan ta yi barci ko kuma ta yanke shawarar ci gaba da kwanciya, ba yana nufin malalaciya bace ko lusara ba; budurwarka ba baiwarka ba ce, ko matarka, don haka ba a wajabta mata aikin mata ba. A daina ji kima."

@keneuoe_ ta amsa:

“Mata a zamanin nan malalata ne. Ina tashi da karfe 3 na asuba, in gasa masara ta yadda lokacin ya farka komai ya shiryu daidai. Na fara share gida da misalin karfe 5:30 na safe, na yi masa wanki, sannan na yi guga. Yana wanka na wanke motarsa sannan na tabbatar karinsa ya kammala kan ya gama wanka."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa ta yi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89, ta bayyana dalili

Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta

A wani labarin, wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.

Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.

Ana dai yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas kuma ana sa ran za a yi masa dashen koda ne a karshen watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.