Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, Ta Ayyana Kyandar Biri a Matsayin Wanda Ke Bukatar Daukin Gaggawa a Duniya
- Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta ayyana Kyandar Biri a matsayin cutar da ke bukatar daukan matakin gaggawa kanta a duniya
- Tedros Ghebreyesus, shugaban WHO ne ya sanar da hakan ranar Asabar inda ya ce cutar na bazuwa ta sabbin hanyoyin da ba a gama ganewa ba
- Hukumar kula da cuttuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta fitar da rahotanni da ke nuna mutane 101 sun kamu da cutar ta kyandan biri
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a ranar Asabar ta bayyana cutar Kyandar Biri a matsayin wanda ke bukatar daukin gaggawa a duniya, rahoton The Punch.
Hukumar lafiyar ta Duniya ta ce ta dauki mataki mafi karfi kan cutar da ke yaduwa, hakan yasa kwayar cutar ta zama abin da ke bukatar gaggawa a kasashen duniya.
The Punch ta rahoto cewa kyandar biri, a cewar Cibiyar Kula da Cuttuka Masu Yaduwa, cuta ne mai yaduwa daga daba zuwa dan adam kuma ya bazu a yankuna kusa da dazukan Afirka ta Tsakiya da Yamma.
Kwayar hallita ta 'Monkeypox Virus' wanda ke rukuni daya da sauran kwayoyin cuta irin su 'Smallpox virus' ne ke janyo ta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi, Direkta Janar na WHO, Tedros Ghebreyesus, ya ce an dauki matakin ne saboda bazuwar da kwayar cutar ta Monkeypox virus ke yi.
"Muna da annoba da ke bazuwa a duniya cikin gaggawa, ta sabbin hanyoyin yaduwa, wanda ba mu kammala fahimta ba," in ji Tedros.
"Saboda wannan dalilan, na yanke shawarar cewa bullar kwayar cutar ta Monkeypox abu ne da ke bukatar daukin gaggawa a duniya."
The Punch ta rahoto cewa, a duniya, an samu akalla mutane 16,000 da suka kamu da cutar a kasashe 70 na duniya kawo yanzu, kuma adadin wadanda suka kamu da cutar ya tashi zuwa kashi 77 cikin 100 daga karshen Yuni zuwa farkon Yuli, a cewar alkalluman WHO.
Rahotanni daga Najeriya, a cewar NCDC na nuna cewa an samu mutum 101 da suka kamu da cutar a 2022, wannan shine adadi mafi yawa tun 2017 da cutar da sake bulla.
Muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da cutar ƙyandar biri
Cutar na iya yaduwa ta hanyar mu'amala da mai dauke da cutar, gumi, yawu da abubuwan da mai cutar yake amfani da su kamar makwanci, a cewar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO).
Hukumar kiwon lafiyar ta duniya ta kara da bayyana cewa lokacin bayyanar cutar kyandar biri tsakanin kwanaki shida zuwa 13 ne amma zai iya zama tsakanin kwanaki 5 zuwa 21.
Haka zalika, hukumar ta ce kyandar biri ba ta cika illata mutum ba, amma za ta iya yin kamari ga wasu, kamar yara, mata masu juna biyu ko mutanen dake fama da matsalar garkuwar jiki saboda wasu cutuka daban.
Asali: Legit.ng