Za A Dauke Wutan Lantarki Na Tsawon Awanni 8 A Kano, Katsina Da Jigawa — KEDCO

Za A Dauke Wutan Lantarki Na Tsawon Awanni 8 A Kano, Katsina Da Jigawa — KEDCO

  • Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ta ce zats dauke wutan lantarki na tsawon awanni takwas 8 a jihohin Kano, Katsina da Jigawa ranar Asabar.
  • KEDCO ta ce zata gudanar da gyara a tashar lantarki da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano
  • Kamfanin KEDCO ta ba wa Kwastomomin hakuri ta ce za a dawo Musu da wuta da zarar Sun kammala Gyara

Jihar Kano - Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ta ce zats dauke wutan lantarki na tsawon awanni takwas 8 a jihohin dake karshinta wanda ya hada da Kano, Katsina da Jigawa a ranar Asabar.

Mai magana da yawun Kamfanin KEDCO, Ibrahim Sani Shawai, ya bayyana haka a shafin sa na Tuwita a Ranar Juma’a 22 ga Watan Yuni. Rahoton Aminiya.Daily Trust

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Dan Abacha ya rasa damar takarar gwamna, an zabi wani a madadinsa

Ya ce za a dauke wutar lantarkin ne daga misalin karfe 10AM na safe zuwa 6:30PM na yamma domin gudanar da gyara a tashar lantarki da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

power
Za A Dauke Wutan Lantarki Na Tsawon Awanni 8 A Kano, Katsina Da Jigawa — KEDCO FOTO PUNCH
Asali: Twitter

A sanarwar da kamfanin KEDCO, wanda ke samar da wutar lantarki ga jihohin Kano, Katsina da Jigawa, ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Hakan zai bamu damar gudanar da gyara a tashar lantarki da ke Kumbotso, wadda ke ba wa Kano wutar lantarki.
“Gyaran da za a yi zai inganta samuwar wutar lantarki ga abokan huldarmu,”

Kamfanin KEDCO ta ba kwastomominta hakuri da tabbacin dawo musu da Wutan zarar an kammala gyaran da su ke yi.

Hukumar kula da Hadura FRSC tana son a nada magajin Boboye daga cikin jami’anta

A wani labari Kuma, Ciyaman din hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Bukhari Bello, ya yi kira da a nada sabon shugaban FRSC daga cikin jami’an hukumar maimakon dauko wani daga wajen.

Rahoton Dail Trust Ya bayyana haka ne a wani taro da hukumar FRSC ta gudanar a ranar Alhamis a Abuja inda ya ce

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa