2023: A Tuwita Kadai Peter Obi Zai Ci Zabe, In Ji Fati Mohammad

2023: A Tuwita Kadai Peter Obi Zai Ci Zabe, In Ji Fati Mohammad

  • Fati Mohammad, shahararriyar jarumar Kannywood ta ce dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi kawai zai ci zabe ne a Twitter
  • Jarumar ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga wasu magoya bayan Peter Obi da suka tanka mata bayan ta wallafa cewa ita Atiku Abubakar ta ke goyon baya
  • Fati ta ce magoya bayan jam'iyyar Labour Party sun iya hayaniya a shafin Twitter amma sun manta cewa ba a Twitter ake zabe ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shahararriyar Jarumar Kannywood, Fati Mohammad, ta zolayi magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, kan mabiya da ya ke da shi a dandalin sada zumunta, rahoton Daily Trust.

Jarumar ta zolayi wasu daga cikin magoya bayan Obi a lokacin da ta ci karo da wasu cikinsu masu amfani da shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Atiku: Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya

Fati Mohammad.
2023: A Tuwita Kadai Peter Obi Zai Ci Zabe, In Ji Fati Mohammad. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jarumar ta wallafa rubutu tana cewa:

"Ina tare da Atiku Abubakar," wannan rubutun ya sa mutane da dama sun bata amsa musamman magoya bayan Obi wadanda aka fi sani da "Obidients".

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta bada amsa bayan awanni, inda ta ce:

"Jiya na wallafa wani abu, wasu mutane suna ta martani da cewa sai Peter Obi, yayin da ni ban san wanene Peter Obi ba, don Allah ina tambaya?, wanene Peter Obi, yana takara ne..? Kuma idan yana takarar, takarar me ya ke yi? Yana takarar ciyaman ne ko kansila?"

Wannan rubutun da ta yi bai yi wa magoya bayan Obi dadi ba inda suka rika wallafa maganganu marasa dadi kanta da dan takarar da ta ke goyon baya.

Fati bata gajiya ba ta sake wallafa wani rubutun a Twitter kuma:

"A Twitter kadai Peter Obi zai iya cin zabe saboda magoya bayansa sun san yadda Twitter ke aiki amma suna mantawa ba a shafin Twitter ake zabe ba."

Kara karanta wannan

2023: Ku Dena Yin Sojan Gona Da Sunan Mu, CAN Ta Gargadi Yan Siyasan Najeriya

Jarumar ta shafe fiye da shekaru 20 a masana'antar fina-finan na arewa wato Kannywood.

Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Saka Jaruman Fim A Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka

A wani rahoton, Hauwa Abubakar, da aka fi sani da Hauwa Waraka a Kannywood, ta ce mutane da dama za su tsinduma jarumai a wuta idan suna da dama, Daily Trust ta rahoto.

Waraka, wacce ta bayyana hakan yayin hira da BBC a ranar Alhamis, ta nuna bacin rai kan zargi marasa kyau da mutane ke yi wa jarumai mata.

Jarumai fina-finan wacce aka haifa a Jos kuma ta girma a Kano, ta fuskanci zargin rashin da'a a masan'antar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164