An kama Matashin Da Ya Yi Fashi kwana Daya Bayan An Sako Shi Daga Kirikiri
- An kama wani yaro dan shekara 17, da laifin fasa wani gida kwana daya bayan an sako shi daga gidan yarin Kirirki
- Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya fitar da faifan bidiyo ya nuna matashin yayi fashi
- Small Bottle Suna matashi aka kama da laifin fashi bayan an sako daga kurkuku ya na zama da iyeyen sa ne a unguwar Ajegule dake jihar Legas
Jihar Legas - An kama wani yaro dan shekara 17, da laifin fasa gida, kwana daya bayan an sake shi daga gidan gyaran hali na Kirikiri, inda ya shafe shekaru biyu bisa laifin zama dan kungiyar asiri.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Daukar Dala Babu Gammo: Yadda Dan Najeriya Ya Ajiye Aikin Da Ake Biyansa Miliyan N24, Ya Koma Turai Yin Digirgir
Da yake bayyana bidiyon wanda ake zargin, Hundeyin ya ce,
“An sako wannan matashin mai shekaru 17 daga gidan yari kwanaki biyu da suka wuce bayan ya shafe shekaru biyu a ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Jiya, ya shiga gidan wani mutum kwashe masa kayayyaki masu daraja. makwabta suka kama shi.
Wanda ake zargin a cikin faifan bidiyon ya ce ya shafe shekaru biyu a gidan gyaran hali na Kirikiri kuma an sake shi ranar Juma’a. Ya bayyana sunan sa da ‘Small Bottle’ kuma iyayensa suna zaune ne a unguwar Ajegunle da ke Legas.
Kotu ta sake tasa keyar Akanta Janar da wasu mutane biyu magarkama
A wani labar kuma, Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare tsohon Akanta Janar na kasa Ahmed Idris da wasu mutane biyu a gidan yari har sai an yanke shawara kan batun belinsu, The Nation ta ruwaito.
Mai shari’a J. O. Adeyemi-Ajayi ya bayar da wannan umarni ne bayan Idris, Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman sun ki amsa laifuka 14 da ake zarginsu na karkatar da kudaden al’umma kusan Naira biliyan 109.
Asali: Legit.ng