Shirin 2023: Za mu sasanta da gwamna Wike nan ba da jimawa ba, inji Atiku
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, yana kan kokarin yin sulhu da gwamna Wike
- An samu rikicin cikin gida tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam'iyyar PDP
- Atiku ya yi maganganu da dama a yau, yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin Arise kan batun siyasarsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku ya bayyana cewa tuni ya tuntubi gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, inda ya ce nan ba da jimawa ba masu ruwa da tsakin jam’iyyar za su sasanta tsakaninsu.
Atiku ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise TV.
Dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce:
“Muna tuntubar Gwamna Wike kuma muna tattaunawa da shi kuma na yi imanin cewa nan ba da jimawa ba za mu yi sulhu. A gaskiya ma, ba da dadewa ba, saboda muna magana da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Muna magana da takwarorinsa gwamnoni. Ina da kwarin gwiwa cewa za mu warware rikicin cikin gida mu ci gaba da harkokinmu."
Atiku, wanda ya bayyana Wike a matsayin hamshakin dan siyasa wanda ke da makoma mai kyau a siyasar Najeriya, ya lura cewa bai da matsala da gwamnan, rahoton Vanguard.
A can baya, dama Atiku ya bayyana cewa, babu wani abu kamar tsagin gwamna Wike ko tsagin Atiku a jam'iyyar PDP, duk muradin jam'iyyar suke karewa, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Gida Siyasa SIYASA Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba
A wani labarin, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce bai taba zama fiye da wata guda ba a Dubai bayan lokacin da ya yi karatun digirinsa na biyu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya bayyana hakan ne a yayin hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Juma'a.
Ya ce:
"Babu wani naci da na ke yi wa Dubai. Abu ne kawai na kafafen watsa labarai suka kitsa. Eh, Na tafi Dubai na dan wani lokaci kuma na yi amfani da lokacin na yi digiri na biyu. Wannan shine lokaci mafi tsawo da na yi a Dubai.
Asali: Legit.ng