Kano: Ganduje Ya Bada Kyautan Naira Miliyan 3 Ga Dalibin Da Ya Fi Kowa Cin Maki a JAMB
- Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bada kyautan Naira Miliyan Uku matsayin tallafi ga wani hazikin dalibi, Suyudi Sani, da ya fi kowa cin makin JAMB a Kano
- Dr Mariya Mahmud Bunkure, Kwamishinan Ilimin Manyan Makarantu na Jihar Kano ce ta sanar da hakan inda ta ce tuni Sani ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, BUK
- Baya ga kyautan Naira miliyan ukun, gwamnatin na Jihar Kano za ta dauki nauyin karatun Sani har ya kammala jami'a domin kada ya samu wata tangarda
Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta bada tallafin karatu na Naira miliyan 3 ga wani dan jihar, Suyudi Sani, saboda bajinta da ya nuna a jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare (UTME) inda ya samu maki 303 cikin 400, rahoton Daily Trust.
Da ya ke magana wurin gabatar da kudin, Kwamishinan Ilimin Manyan Makarantu, Dr Mariya Mahmud Bunkure, ta ce Sani ya riga ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, (BUK), kuma ya zo na 7 cikin mutum 774 a bikin bada lambar yabo na 'Young Nigerian Scientist Presidential Awards'.
"Baya ga zama zakara da Suyudi ya yi a bangaren Biology a gasar, ya zo na farko a gasar matasan masu kimiyya a matakin jiha, wanda ya bashi damar shiga gasar na shugaban kasa a mataki na kasa," ta kara da cewa.
Bunkure ta ce nasarar da ya samu a jarrabawar JAMB din yasa Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin tallafa masa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta ce baya ga kudin da aka ba shi, gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatunsa baki daya don tabbatar cewa bai samu tangarda ba.
Bunkure ta kuma ce gwamnatin ta karrama shi domin ya zama abin karfafa gwiwa ga sauran dalibai a jihar.
Ta kara da cewa gwamnatin Ganduje za ta cigaba da mayar da hankali sosai a bangaren ilimi domin yan jihar su rika samun digiri.
Wanda ya samu kyautar ya gode wa gwamnatin jihar ya kuma yi alkawarin zai mayar da hankali a karatunsa.
Ganduje Ya Yi Wa Babachir Lawal Martani: Gidauniya Ta Bata Taba Tilastawa Kirista Karbar Musulunci Ba
A bangare guda, Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi watsi da ikirarin da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi na cewa ana amfani da Gidauniyar Ganduje don tilastawa Kirista karbar Musulunci.
Yayin da ya ke nuna kin amincewarsa da zabin Kashim Shettima a matsayin mataimakin Asiwaju Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, Lawal ya yi zargin Ganduje na neman musuluntar da Najeriya.
Asali: Legit.ng