Matsalar Tsaro: Kashi 70 na wadanda aka kashe a watan Yuni a Arewa suke
- Bincike ya nuna fiye da kashi 70 na wadanda aka kashe a Najeriya a watan Yuni mazauna yankin Arewa ne
- Beacon Consulting Limited ta ce Jihar Sokoto ne kan gaba wajen sace-sacen mutane a fadin kasar
- An kashe mutane 765 a kananan hukumomi 185 da ke jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja a watan Yuni
Najeriya - Wani Bincike game da harkar tsaro a Najeriya ya nuna kashi 75 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga a watan Yuni a Arewacin Najeriya suke, rahoton BBC
Sabuwar binciken da kamfanin Beacon Consulting Limited ta fitar akan harkar tsaro na watan Yuni, ya nuna cewa an kai harin yan bindiga sau 338 a fadin kasar kuma an sace mutane 651.
Kuma an kashe mutane 765 a kananan hukumomi 185 dake jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja.
Binciken sun bayyana cewa kashi 28 na kashe-kashen sun faru ne a Arewa maso Gabas inda aka kashe mutum 219, sai kashi 23 a Arewa ta Tsakiya inda aka kashe mutum 180, kashi 23 a yankin Arewa maso Yamma ne inda aka kashe mutane 180.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashi 10 na kashe-kashen ya faru ne a Kudu maso Yamma inda aka kashe mutum 80, yankin Kudu maso Gabas na da kashi 9 inda kashe mutum 70, SaI kuma Kudu maso Kudu inda aka kashe mutum 36.
Binciken ya nuna kashi 75 na mutanen da aka kashe a watan Yunin 2022 na zaune ne a arewacin Najeriya,.
A game da satar mutane kuma, Jihar Sokoto ne kan gaba da mutum 107 sai jihar Kaduna inda aka sace mutum 92, sai jihar Katsina inda aka sace mutum 90.
Sauran su ne Neja inda aka sace mutum 60, an sace mutum 56 a Zamfara, yayin da aka sace mutum 56 a Abuja, da kuma mutum 47 a Borno.
Masari ya raba kayan tallafi ga mutanen da yan bindiga suka kai wa hari a Safana
A wani labari kuma, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya raba kayan agajin gaggawa ga wadanda ‘yan fashi suka kai wa hari a karamar hukumar Safana da ke jihar. Rahoton Daily Trust
Kayayyakin da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan N21 sun hada da kayan abinci, tabarmu, sabulun wanka da dai sauransu.
Asali: Legit.ng