Masari ya raba kayan tallafi ga mutanen da yan bindiga suka kai wa hari a Safana

Masari ya raba kayan tallafi ga mutanen da yan bindiga suka kai wa hari a Safana

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya raba kayan agajin gaggawa ga wadanda ‘yan fashin suka kai wa hari a karamar hukumar Safana
  • Yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Safana makonni biyu da suka wuce inda suka kashe mutane da dama ciki har da babban dan sanda
  • Gwamna Masari ya jajantawa iyalan wadanda harin yan bindiga ya rutsa da su tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya raba kayan agajin gaggawa ga wadanda ‘yan fashi suka kai wa hari a karamar hukumar Safana da ke jihar. Rahoton Daily Trust

Kayayyakin da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan N21 sun hada da kayan abinci, tabarmu, sabulun wanka da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Ban dai ji dadi ba: Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe malamin Kirista a Kaduna

An raba su ne ga iyalai a garuruwa biyar a karamar hukumar, da suka hada da, Zakkah, Sabon Garin Gamji, Kunamawa, Kukar Rabo da Tsaskiya.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a karamar hukumar Safana, inda suka kashe mutane da dama ciki har da kwamandan ‘yan sanda na yankin Dutsinma, ACP Aminu Umar.

Masari
Masari ya raba kayan tallafi ga mutanen da yan bindiga suka kai wa hari a Safana - FOTO DAILY TRUST
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin rabon, Gwamna Masari wanda ya samu wakilcin shugaban karamar hukumar Safana Muhammad Kabir Umar, ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayan agajin tare da yin addu’ar Allah ya dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da iyalan wadanda aka kashe da wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, da wadanda suka samu raunuka sakamakon harin, da kuma wadanda aka sace musu shanu.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun cafke wasu Malamai saboda sun yi korafi a kan Shugaban NARICT

Sauran wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da wasu mutane da ke karbar magani a cibiyar kula da lafiya ta tarayya sakamakon kuskuren bam din da jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya jefa a kauyen Kunkunna.

An Kashe Daya Daga Cikin Limaman Katolika Biyu Da Aka Sace A Kaduna

A wani labari kuma, Masu garkuwa da mutane sun kashe Reverend Fada John Cheitnum, daya daga cikin limaman cocin Katolika guda biyu da aka sace a karamar hukumar Lere (LGA) ta jihar Kaduna. Rahoton Channels

Wanda aka kashe, shi ne Daraktan Sadarwa na cocin Katolika reshen Kafanchan, da kuma Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a karamar hukumar Jema’a ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel