'Yan bindiga sun kai hari wata Jami'a a Najeriya, sun shiga Hostel ɗin Mata

'Yan bindiga sun kai hari wata Jami'a a Najeriya, sun shiga Hostel ɗin Mata

  • Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari wata jami'ar kuɗi a jihar Kuros Riba da daren jiya Talata, sun sace ɗaliba ɗaya
  • Bayanai sun tabbatar da cewa maharan sun tare ɗalibai mata da ke kan hanyar komawa Hostel daga ajin karatu, sun jikkata wasu
  • Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa kwamishina ya tura dakaru domin dawo da doka da oda da ceto wacce aka sace

Cross River - Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗaliba mace a jami'ar kuɗi Arthur Jarvis University da ke ƙaramar hukumar Akpabuyo a jihar Kuros Riba.

Hukumomin Jami'ar a wata sanarwa sun tabbatar da faruwar lamarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 10 a jihar arewa

Arthur Jarvis University
'Yan bindiga sun kai hari wata Jami'a a Najeriya, sun shiga Hostel ɗin Mata Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwan, wacce muƙaddashin Rijistara ta jami'ar, Misis Ughas Ngozi, ta fitar ta bayyana cewa tuni jami'an tsaro suka shawo kan lamarin.

Daily Trust ta rahoto sanarwan na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugabannin jami'a sun maida hankali kan abun da ya faru kuma hukumomin tsaro sun kwace iko da makarantar, saboda haka muna rokon baki ɗaya ɗalibai da ma'aikata sun kwantar da hankulan su kuma su cigaba da harkokin su."

Budu da ƙari, sanarwan ta gargaɗi mutane da su guji yaɗa labaran ƙarya kan abin da ya faru.

Me yan bindigan suka aikata a jami'ar?

Wasu majiyoyi daban-daban sun tabbatar da cewa Ɗaliban da harin ya shafa na kan hanyar su ta komawa ɗakunan kwana daga wurin karatu, ba zato yan bindigan suka tare su kuma suka yi awon gaba da ɗaliba ɗaya.

Sauran ɗaliban da suka tsira daga harin sun ji raunuka kala daban-daban a harin, a cewar majiyoyin da aka tattara.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun saki sabon Bidiyo, sun bayyana wuraren da zasu zafafa hare-hare a Najeriya

Wane mataki jami'an tsaro suƙa ɗauka?

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ya ce kwamishinan yan sanda, Aminu Alhassan, ya tura jami'an yaki da garkuwa, yaƙi da yan asiri domin dawo da doka da oda da kuma ceto ɗalibar da aka sace.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sama da 100 sun kai kazamin hari jihar Katsina da tsakar rana, sun aikata mummunar ɓarna

Miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a yankin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina da tsakar ranar Talata.

Mazauma yankunan sun tabbatar da cewa mutane 6 sun rasa rayuwarsu a harin, wasu kuma na kwance a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262