Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

  • Wani jigon jam’iyyar APC da wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi garkuwa da shi a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli ya tsallake rijiya da baya
  • An yi garkuwa da jigon na APC mai suna Mista Godwin Aigbogun a jihar Edo a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga gonarsa
  • An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansa inda suka bukaci a biya shi Naira miliyan 5 domin su sake shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban jam’iyyar APC gunduma ta 9 a karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo, Mista Godwin Aigbogun, ya kubuta daga maboyar wadanda suka sace shi.

Masu garkuwa da mutanen da ake zargin Fulani makiyaya ne, an ce sun bukaci iyalansa da su biya Naira miliyan 5, bayan da aka yi garkuwa da shi a hanyarsa ta komawa kauyensu daga gonarsa da ke Ologbo-nugu a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Hanyarsa Ta Dawowa Da Gonarsa

Yadda jigon APC ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Yanzu-Yanzu: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sakataren Yada Labarai na Jihar Barista Peter Uwadiae, ya tabbatar wa da jaridar Punch cewa jigon ya tsere ne da safiyar Laraba kuma ya ce tuni ya koma ga iyalansa.

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zan iya tabbatar muku da cewa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane. Ban san yadda ya yi ba amma dole ne in yaba masa da irin jarumtarsa. Ahalin jam’iyyar APC na jihar sun yi farin ciki da hakan. Yanzu yana tare da ahalinsa.”

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman Katolika 2 a Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da Limaman darikar Katolika guda biyu, Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Chietnum ya kasance shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jiha, yan sanda sun ce ba zata saɓu ba

Da yake tabbatar da lamarin, Kansilan darikar Katolika a Kafancha, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli, ya ce miyagun sun yi awon gaba da limaman ne a ranar Juma’a, Channels TV ta rahoto.

Okolo ya ce:

“Cike da radadi muke sanar maku da labarin sace limamanmu biyu, Rev. Frs. John Mark Cheitnum da Donatus Cleopas."

Dakarun Najeriya sun samu sa’a, sun bindige ‘Dan bindigan da ya addabi Kaduna

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya da ke yakar ta’addanci a jihar Kaduna, sun yi nasarar harbe wani hatsabibin ‘dan bindiga da ya yi suna a yankin Chikun.

Kamar yadda Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi a jiya, an yi kicibis da ‘dan bindigan ne a wajen Kidunu.

Mista Samuel Aruwan ya ce an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da miyagun ‘yan bindigan. Daily Trust ta ce Kwamishinan ya fitar da wannan jawabi ne a ranar Talata, 19 ga watan Yuli 2022, aka tabbatar da nasararori da jami’an tsaron suka samu.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya yi ganawar sirri da fitaccen fasto kan batun Shettima

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.