ASUU: Da 'ya'yan 'yan siyasa ne a jami'o'in gwamnati, da yajin mu ba zai kai kwana biyu ba
- Malaman jami’o’i a karkashin inuwar ASUU sun mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari martani kan wa’adin makwanni biyu da ya baiwa ministan ilimi na daidaita yajin
- Malaman jami’ar sun ce nan da kwanaki biyu za su koma aiki idan da gwamnatin tarayya ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar
- Shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke, ya kara da cewa idan da ‘ya’yan ‘yan siyasa ne a jami’o’in gwamnatin Najeriya, yajin ba zai dauki kwanaki biyu ba za a magance shi
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ce idan da ‘ya’yan ‘yan siyasa ne ke halartar jami’o’in gwamnatin Najeriya, yajin aikin kungiyar ba zai shafe kwanaki biyu ba.
Kamar yadda shafin jaridar The Cable ta ruwaito, kungiyar ta bayyana cewa wa'adin makwanni biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministan ilimi Adamu Adamu ya yi yawa.
Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, yayin da yake hira da gidan talabijin na Channels.
ASUU ta shafe kwanaki 156 a yau tana yaji
A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman ta shiga yajin aikin saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cika wata yarjejeniya kan batutuwan da suka shafi kudaden jami’o’i, albashi da alawus-alawus na malamai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministan ilimi, Adamu Adamu wa’adin makwanni biyu ya warware matsalolin da ke tsakanin gwamnati da ASUU.
ASUU tayi magana akan shirinta na komawa kan aiki
Da yake magana kan wa’adin, Osodeke ya ce makwanni biyu “sun yi tsayi sosai”, yana mai cewa kungiyar za ta iya janye yajin aikin cikin kasa da kwanaki biyu idan gwamnati ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar.
A cewarsa:
“Makwanni biyu sun yi tsayi da yawa. Batun sake sasantawar bangarorin biyu ya kammala, wanda ke nufin cewa daya ya tafi."
Osodeke ya kara da cewa yayin da wutar rikici ta tashi a gida, kudi ake nemowa don magance rikicin kamar yadda ake nemowa wasu abubuwan daban.
Gwamnatin Najeriya ta shahara wajen karbo rancen kudade don magance matsaloli, amma ta gaza karbo rancen don magance matsalar da bangaren ilimi ke fuskanta.
Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce ba wai kawai ta na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi a halin yanzu bane, a’a, tana ma kokarin kawar da yajin aikin da kungiyar ke yi ne har zuwa nan gaba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a taron koli karo na 81 na kwamitin ba da shawara kan harkokin ilimi (JCCE) da aka gudanar a Yola jihar Adamawa, The Nation ta ruwaito.
Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo, wanda ya zanta da manema labarai a gefen taron, ya jaddada cewa ana ci gaba da daukar matakai domin bai kamata ace ASUU ta sake yajin aiki a nan gaba ba.
Asali: Legit.ng