Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi
- Umar Sani ya gurfana a gaban kuliya bayan ya sace janareto da kayan wuta a wani masallaci da ke garin Yola, jihar Adamawa
- Jami'an yan sanda sun damke Sani wanda ya tattara kayan Masallaci ya kuma ci kasuwarsu tare da sheke kudin akan tabar wiwi
- Alkali Hon. Muhammad Alamin Diya Lamurde ya jefa matashin gidan yari har zuwa ranar da za a sake zama a watan Agusta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Adamawa - Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai suna Umar Sani sannan ta gurfanar da shi kan zargin satar injin janareto da lasifikan wani Masallaci a Yola, babban birnin jihar.
An gurfanar da Umar a gaban kotun II na yankin Jimeta karkashin jagorancin Hon. Muhammad Alamin Diya Lamurde, a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, LIB ta rahoto.
Yayin da yake tsare, wanda ake zargin ya tona cewa shi da dan mai anguwarsu ne suka farmaki Masallacin Rumde Baru a ranar Lahadi da misalin 12:00, lokacin babu kowa a Masallacin.
Ya yi bayanin cewa sun yi awon gaba da kayayyakin (Janareto, lasifika da sauran kayan wuta), sun kuma siyar da kowanne kan N6,000 sannan suka kashe kudin kan tabar wiwi tare da abokai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Mun kashe duka kudaden da aka samu akan tabar wiwi," in ji shi.
Rahoton ya kara da cewa dan sanda mai gabatar da kara, Cpl Ismail, ya sanar da alkalin kotun, Hon. Alamin Lamurde cewa jami’an yan sandan yankin Jambutu ne suka kama wanda ake karan.
Wanda ake karan ya kuma amsa laifinsa sannan kotu ta yi umurnin tsare shi a gidan yari sannan ta dage zaman zuwa 2 ga watan Agusta domin cigaba da shari’a kamar yadda mai gabatar da kara ya nema.
Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo
A wani labarin kuma, rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman gogarmar dan bindiga, Ado Aleru, wanda Sarkin Yandoto na Zamfara ya nadawa sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar ruwa a jallo.
Ana neman Aleiro ne kan zargin aikata ayyukan ta’addanci ciki harda kashe akalla mutane 100, jaridar Vanguard ta rahoto. '
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, kan nadawa dan ta’addan da ake nema ruwa jallo sarauta.
Asali: Legit.ng