Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Hanyarsa Ta Dawowa Daga Gonarsa
- Wasu bata gari da ake zargin masu garkuwa ne sun sace shugaban APC na gundumar Ugu a karamar hukumar Orhionmwon a Edo
- Wani jigon jam'iyyar ta APC ya tabbatar da sace Godwin Aigbogun yana mai cewa abokansa na siyasa ne suka sanar da shi
- Kakakin yan sandan Jihar Edo, Jenifer Iwegu, ta ce an sanar da su afkuwar lamarin kuma tuni sun tura jami'ai domin bincika dazukan garin da nufin ceto wanda aka sacen
Edo - Ana zargin wasu bata gari sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC ta Gundumar Ugu a karamar hukumar Orhionmwon ta Jihar Edo, Godwin Aigbogun.
Wani jigo na jam'iyyar ta APC a Ugu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu abokansa na siyasa suka sanar da shi faruwar lamarin, Punch ta rahoto.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An sanar da shi cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun sace shugaban APC na Gundumar Ugu (9) a ranar Litinin a hanyarsa na dawowa daga gonarsa a kauyenmu, Ologbonugu."
Abin da yan sanda suka ce game da lamarin
Jami'ar hulda da mutane na rundunar yan sandan jihar, Jennifer Iwegu, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ta tabbatar da sace jigon na APC.
Wani sashi na sanarwar:
"Rundunar yan sandan Jihar Edo, a ranar 18 ga watan Yulin 2022 misalin karfe 8.52 na dare, ta samu korafi daga wani Godwin Erhahon na kauyen Ologbounu a karamar hukumar Orhionmwon ta Jihar Edo, cewa wasu bata gari da ake zargin masu garkuwa ne sun sace dan uwansa."
Kakakin yan sandan ta ce bayan samun korafin an tura jami'ai na sashin yaki da garkuwa sannan take sun kuma tafi bincika dazuka da nufin ceto shi da kama masu garkuwar.
Ta bukaci mazauna garin su kwantar da hankalinsu yayin da rundunar ke kokarin gano inda ya ke ta kuma ceto shi tare da kama miyagun.
Yan Bindiga Sun Kutsa Gonar Tsohon Gwamna a Najeriya, Sun Sace Mai Kula Da Gonar
A wani rahoton, yan bindiga sun sace Christopher Bakare, mai kula da gonar marigayi tsohon gwamnan Jihar Oyo, Otunba Alao Akala.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sace Bakare ne a yammacin ranar Asabar a gidan gona na TDB da ke Jabata, karamar hukumar Surulere na jihar.
Asali: Legit.ng