'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Edo, yan sanda sun bazama
- Masu garkuwa da mutane ɗauke da makamai sun yi awon gaba da shugaban APC na gunduma ta 9, ƙaramar hukumar Orhionmwon, jihar Edo
- Wata majiya daga cikin iyalan ɗan siyasa, ya bayyana cewa sun nemi a haɗa musu miliyan N5m a matsayin fansa kafin su sako shi
- Hukumar yan sanda ta ce ba zata saɓu ba yayin da jami'ai suka bazama cikin jeji don kubutar da shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Edo - 'Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban jam'iyyar APC na gunduma ta 9, ƙaramar hukumar Orhionmwon, a jihar Edo, Mista Godwin Aigbogun.
Rahoton da Daily Trust ta haɗa ya nuna cewa masu garkuwan sun nemi a tattara musu kuɗi miliyan N5m a matsayin fansa kafin su sako shi.
Ɗaya daga cikin mamban iyalan gidan su, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilin jaridar cewa masu garkuwan sun fara tattaunawa da iyalan wanda suka sace ta wayarsa.
"Sun tuntuɓi iyalansa kuma suna buƙatar kudi miliyan N5m na fansa kafin su sako shi ya koma gida," inji majiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa Yan Sakai tare da haɗin guiwar Jami'an tsaro sun bazama cikin jeji domin kuɓutar da ɗan siyasan.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Aigbogun, ɗan shekara 54 a duniya, shi ne shugaban APC na gundumar Ugo ta 9 kuma ya shiga hannun masu garkuwa ranar Litinin a yankin Ologbo-nugu a hanyarsa ta komawa gida daga gona.
Maharan sun fito ba zato daga cikin jeji kuma suka tilasta motarsa ta tsaya sannan suka tasa keyarsa zuwa inda ba'a sani ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar yan sandan Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da sace ɗan siyasan amma ya ce ba shi da masaniya game da fansar da suka nema.
Chidi ya ƙara da cewa Dakarun yan sanda masu yaƙi da garkuwa da mutane sun mamaye dazuka da nufin kubutar da mutumin cikin koshin lafiya da kuma yuwuwar damƙe masu garkuwan.
Ƴa roki mutane su kwantar da hankalin su don kada su dawo da hannun agogo baya a kokarin da jami'ai ke yi na ceto shugaban APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A wani labarin kuma wani Saurayi ya ga takansa, yayin da daga zuwa sayo wa budurwarsa Shawarma, ita kuma ta sace motarsa a Kano
Wata budurwa ta shiga hannun dakarun yan sanda bisa zargin sace Motar Saurayinta a Kofar Fanfo da ke cikin birnin Kano.
Saurayin ya bayyana cewa daga zuwa sayo mata Shawarma da ya dawo ya taras ba motar kuma ba labarinta a wurin.
Asali: Legit.ng