2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

  • Matasan Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN sun nuna rashin amincewarsu da tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi a 2023
  • Kungiyar ta bakin shugabanta na yankin arewa maso tsakiya, Owoyemi Olusola ne ta bayyana hakan yana mai cewa ba za su goyi bayan raba kan kasa ba
  • Olusola ya ce umurci dukkan matasan kirista a Najeriya da takwarorinsu na wasu addinai su yi rajistan zabe kuma su tabbatar ba su zabi wadanda za su raba kan kasa ba

FCT, Abuja - Kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, reshen matasa ta ce babu yadda za ta yi ta bari mambobinta su zabi musulmi da musulmi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, rahoton Vanguard.

Shugaban kungiyar, yankin arewa ta tsakiya, Owoyemi Alfred Olusola, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Abuja a ranar Talata, ya ce matasan kirista sun yanke shawarar ba za su goyi bayan hakan ba.

Kara karanta wannan

Abdullahi Adamu: Ba za mu iya tilastawa kowa zama ko ficewa daga APC ba

Tinubu da Shettima.
2023: Ba Za Mu Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, Matasan Kungiyar CAN. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Duk mun san cewa a watanni da suka shude, kafafen watsa labarai na Najeriya da yan kasan suna ta tattaunawa kan batun tikitin musulmi da musulmi da APC, daga cikin jam'iyyun siyasar kasar ta yi gabanin babban zaben 2023.
"Muna son mu bayyana karara cewa hakan ba abu mai kyau bane ga Najeriya, musamman yanzu da ake fuskantar rashin tsaro. Duk wani dan takara na gari zai lura da batun tafiya tare da bangarorin tarayyar.
"Matasan kirista na Najeriya suna sane da cewa siyasar Najeriya ta dauki zafi, don haka, ba za mu goyi bayan duk wani mataki da zai sake raba kan mutane da cinna wa kasar wuta ba."

Kungiyar matasan kiristan ta cigaba da cewa:

"Tikitin musulmi da musulmi na shugaban kasa raina wa yan kasa hankali ne kuma matasan kiristoci suna cewa a A'a!

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

"Duk da mun san cewa yan takara na da damar yin zabinsu, saboda hadin kan kasa, ya kamata jam'iyyun su rika kula da abin da ke faruwa su kuma yi duk abu mai yiwuwa don kada su raba kan yan Najeriya.
"YOWICAN ta yi kira ga dukkan matasan kiristoci masu son zaman lafiya da takwarorinsu na wasu addinai kada su bari a siye su, su amshi abin da ba zai hada kai da kawo cigaba a Najeriya ba."

Daga karshe kungiyar ta yi kira ga dukkan matasa su yi rajitsa su tattaro yan uwansu su kayar da duk wata jam'iyya da za ta kawo rabuwan kasa, a dora gwamnati wacce za ta hada kan yan kasa ta kawo zaman lafiya.

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

A baya, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bawa kiristoci tabbacin cewa babu abin tsoro game da tikitin musulmi da musulmi na Sanata Kashim Shettima da Asiwaju Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole

Ya ce zabin musulmi da musulmi na jam'iyyar a zaben shugaban kasar "kaddara ce ta Allah."

Adamu ya yi wannan jawabin ne a Daura lokacin da ya jagoranci Kwamitin Ayyuka na Jam'iyyar yayin ziyarar Sallah da suka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164