Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya ba ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin ASUU

Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya ba ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin ASUU

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin kawo karshen yajin aikin ASUU nan da makwanni biyu kacal
  • Ministoci da masu ruwa da tsaki a Najeriya sun gana da Buhari, sun bayyana masa halin da ake ciki game da ASUU
  • Malaman jami'a sun shafe watanni akalla hudu suna yajin aiki saboda rashin samun cikakken abin da suke bukata

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware matsalar yajin aikin da kungiyoyin ma'aikatan jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makwanni biyu, Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi wasu bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin na jami’o’i da gwamnati.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

Buhari ya umarci a kawo karshen yajin aikin ASUU
Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya ba ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin ASUU | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kun ji cewa, ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran kungiyoyi su ma suka tsunduma bayan ganin rashin daidaiton sakamako da gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu.

Sauran kungiyoyin uku da suka fara yajin aikin sun hada da kungiyoyin ma'aikata na SSANU, NASU da kuma NAAT.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya kira taron jin ta bakin masu ruwa da tsaki

Shugaba Buhari ya kira taron na ranar Talata ne domin karbar bayanai daga tawagar gwamnati kan yajin aikin da ya dauki tsawon lokaci ana yi.

Bayan jin ta bakin masu ruwa da tsaki na hukumomin da abin ya shafa, Buhari ya umurci Ministan Ilimi da ya tabbatar da cewa an warware matsalar cikin makwanni biyu tare da kawo masa rahoto.

Wadanda za su tabbatar da kawo karshen yajin ASUU

Kara karanta wannan

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

Majiyoyi a taron sun kuma ce shugaba Buhari ya ba da umarnin cewa ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya kasance a duk wani taron da za a yi domin warware batun.

Majiyar ta ci gaba da cewa, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha zai kasance cikin tawagar da za ta tunkari kungiyoyin da ke yajin aikin.

Daya daga cikin majiyoyin, ta ce shugaban kasar ya yabawa Ngige a kokarinsa na ganin an shawo kan lamarin.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Ilimi, Mallam Adamu, Ministan Kudi, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Dakta Zainab Ahmed da Ministan Kwadago da Aiki, Sanata Ngige.

Hakazalika da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Farfesa Isa Ali Pantami, Shugabar ma’aikata ta tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan, shugaban hukumar albashi da kudaden shiga na kasa, Ekpo Nta da babban daraktan kasafin kudi, Ben Akabueze.

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce ba wai kawai ta na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi a halin yanzu bane, a’a, tana ma kokarin kawar da yajin aikin da kungiyar ke yi ne har zuwa nan gaba.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a taron koli karo na 81 na kwamitin ba da shawara kan harkokin ilimi (JCCE) da aka gudanar a Yola jihar Adamawa, The Nation ta ruwaito.

Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo, wanda ya zanta da manema labarai a gefen taron, ya jaddada cewa ana ci gaba da daukar matakai domin bai kamata ace ASUU ta sake yajin aiki a nan gaba ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.