Yan Bindiga Sun Kutsa Gonar Tsohon Gwamna a Najeriya, Sun Sace Mai Kula Da Gonar
- Wasu masu garkuwa da mutane sun sace Christopher Bakare, mai kula da gonar marigayi Otunba Alao Akala tsohon gwamnan Jihar Osun
- Wata majiya daga iyalan Bakare ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa masu garkuwan sun nemi a biya su Naira Miliyan 100 kudin fansarsa
- Kanal Olayinka Olayanju (mai ritaya), kwamandan hukumar tsaro ta yankin yammacin Najeriya wanda aka fi sani da Amotekun ya ce bai da labarin afkuwar lamarin
Jihar Oyo - Yan bindiga sun sace Christopher Bakare, mai kula da gonar marigayi tsohon gwamnan Jihar Oyo, Otunba Alao Akala.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sace Bakare ne a yammacin ranar Asabar a gidan gona na TDB da ke Jabata, karamar hukumar Surulere na jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani majiya daga iyalansa sun shaida wa wakilin majiyar Legit Hausa cewa yan bindigan sun tuntubi iyalan sun nemi a biya Naira miliyan 100 don fansarsa.
Majiyar ta ce:
"Eh, an yi garkuwa da shi. Suna magana da harshen yarbanci sama-sama. A gonar aka sace shi. Muna ta kokarin tattaunawa da su duk da cewa an sanar da yan sanda."
Martanin Rundunar Amotekun
Da aka tuntube shi, kwamandan rundunar tsaro ta yankin yammacin Najeriya, WNSN, da aka fi sani da Amotekun, Kanal Olayinka Olayanju (mai ritaya), ya ce bai da masaniya kan afkuwar lamarin.
An Yi Awon Gaba Da Shugaban CAN Da Abokin Aikinsa A Kaduna
A wani rahoton, Cocin Darikar Katolika ta Kafanchan, Jihar Kaduna, ta sanar da sace Rabaran Fada John Cheitnum da Rabaran Fada Donatus Cleopas, rahoton Daily Trust.
Chietnum shine shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya wato CAN, reshen karamar hukumar Jama'a ta Jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa, shugaban cocin reshen Jema'a, Rabaran Fada Emmanuel Okolo, ya ce an sace limaman cocin biyu ne a ranar Juma'a a gidan fastoci da ke Christ the King Catholic Church, Yadin Garu, karamar hukumar Lere.
Asali: Legit.ng