Bidiyo: Dangote ya halarci nadin sarautar matar marigayi Abba Kyari matsayin Gimbiyar Jama'are
- Alhaji Nubu Wabi III, Sarkin Jama'are ya nada matar marigayi Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin Gimbiyar Jama'are
- An yi bikin nadin sarautar a ranar Lahadi a fadar basaraken inda har biloniya Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta
- Wabi ya kwatanta Hajiya Kulu da mace jaruma tagari mai kishin al'umma da don ganin cigaban Jama'are
Bauchi - Sarkin Jama'are, Mai martaba Alhaji Nuhu Wabi III, ya nada matar marigayi tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin gimbiyar farko ta Jama'are.
A bikin nadin sarautar da aka yi a fadarsa ranar Lahadi, sarkin ya kwatanta ta da diya tagari a Jama'are wacce ta yi matukar kokari wurin kawo cigaba ga dukkan masarautar.
Marigayi Kyari 'dan asalin jihar Borno ne amma matarsa Hauwa Nee Gidado ta fito daga garin Jama'are dake karamar hukumar Jama'are ta jihar Bauchi.
"A al'adance Gimbiya 'yar sarki ce kuma ita ce gadar dake tsakanin sarki da mata wadanda basu da damar shiga lamurran masarautar kai tsaye.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Da wannan nadin, matan Jama'are a yanzu suna da wakiliya a majalisar zartarwa ta masarautar, za a ji muryoyinsu tangaran.
"Burina ya cika saboda ina da diyar masarautar a majalisar zartarwarta," yace.
Wabi ya kwatanta Hauwa a matsayin mace jaruma wacce ta damu da damuwar jama'a tare da cigaba masarautar.
"Ta cancanci sarauta saboda ta mallaki dukkan dalilai uku da ya dace a karramata a Jama'are,"yace
Fitaccen biloniyan duniya, AlhajiAliko Dangote, ya samu damar halartar nadin sarautan. @arewafamilyweddings ne suka wallafa bidiyon.
Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe
A wani labari na daban, an yi wa rikakken dan ta'adda Ado Aleru, nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.
'Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta kirkiro a watan Mayun da ya gabata.
An kirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa.
Hukuncin bai wa shugaban 'yan bindigan sarauta ya biyo baya ne sakamakon kokarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da 'yan ta'addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.
Asali: Legit.ng